Rahotanni dake shigo mana yanzu daga Jihar Sokoto na bayyana cewar an toshe layukan sadarwa a jihar fiye da mako biyu bayan an toshe hanyoyin sadarwar a jihar Zamfara da ke makwaftaka da Jihar.
Gwamnatin jihar ta tabbatarwa BBC da matakin, inda kakakin gwamnan jihar Muhammad Bello ya ce an toshe layukan ne a ?ananan hukumomi 14 na jihar.
Wasu mutanen jihar sun ce idan an kira layukan MTN ba a kamawa, wasu kuma sun ce matsalar ta shafi har da masu amfani da layin Airtel.
Matakin toshe layukan na sadarwa ya shafi yankunan jihar Katsina da ke makwabtaka da jihar Zamfara.
Hukumomin jihohin sun ce an ?auki matakin domin ?o?arin magance matsalolin ?an bindiga masu kai hare-hare da satar mutane a jihar.
Toshe layukan na zuwa bayan wasu ?an bindiga sun abka garin Tangaza sun kashe mutane tare da satar abinci.
