Rahotanni dake shigo mana yanzu daga birnin Kano na bayyana cewar wasu gungun Matasa sun hallaka Matashi Muhammad Suleman a daren jiya sannan suka yi awon gaba da wayarshi.
Rundunar yan sanda ta jihar Kano ta tabbatar da mutuwar matashin mai suna Muhammad Suleman da ake zargin wasu Matasa suka kashe tare da kwace masa waya.
Yan sandan sun ce an kashe matashin ne a lokacin da yake kan hanyarsa ta komawa gida tare da iyalinsa matasan suka tasar masa a kan titiun Yahaya Gusau a dare jiya
Rundunar ‘Yan Sandan ta tabbatar da zata cigaba da fadada bincike domin zakulo gami da kamo miyagun da suka yi wannan aika aika domin fuskantar hukunci.
