Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Rundunar ‘Yan Sandan Jihar ta bayyana cewa ta dam?e gaggan masu laifi har 25 tare da makamai tsakanin watan Agusta da Satumba.
Kakakin Ya?a Labarai na ‘Yan Sandan Kaduna, Muhammad Jalige ne ya bayyana haka a ranar Alhamis, a lokacin da ya ke wa manema labarai bajekolin masu laifin, a hedikwatar ‘yan sandan jihar, a Kaduna.
Ya ce an kama su ne bayan sun aikata muggan laifuka da su ka ha?a da fashi da makami, kisan kai, garkuwa da mutane, ayyukan ?ungiyoyin asiri, mallakar muggan makamai da sauran laifuka daban-daban.
Daga cikin wa?anda aka kama har da wa?anda su ka ha?a kai su ka dira gidan direban jirgin sama, kuma ?an Sanata Bala Ibn Na-Allah, wato Abdulkareem Na-Allah, su ka kashe shi a cikin gidan sa.
Sun dira gidan sa cikin dare a ranar 26 Ga Agusta, su ka kashe shi, kuma su ka tsere da wasu kayayyakin sa, ciki kuwa har da motar sa.
Jalige ya ce an samu makamai samfuran bindigogi daban-daban a hannun masu aikata muggan laifukan, wa?anda yawanci duk sun amsa laifin su.
Ya ce da an gama bincike za a dam?a wa kotu su, domin hukunta su daidai da laifukan da su ka aikata.
