Rundunan yan sandan jahar Adamawa tace tayi nasaran kama mutane dubu daya da dari daya da tamanin da hudu tun daga ran 11-1-2021 zuwa yanzu bisa zarginsu da aikata laifuka daban daban a fadin jahar Adamawa.
Kwamishina yan sandan jahar Adamawa CP Aliyu Adamu Alhaji ne ya baiyana haka a lokacin da yake gabatarwa manema labarai wadanda ake zargin a shelkwatar rundunŕn dake yola.
Kwamishinan yace tun da ya fara aiki a matsayin kwamishinan yan sanda a jahar ta Adamawa rundunan ta nasara sosai wajen daki aiyukan bata gari a cikin al umma.
Har wayau kwamiahinan ya rundunan a ahirye take ta cigaba da gudanar da aiyukanta domin kare rayuka dama dukiyoyin al umma baki daya.
Cikin mutane dubu da dari daya da tamanin da hudu da aka kama dai tunin an yankewa mutane dari hudu da sittin hudu hunkunci a yayida mutane dari bakwai da shirin kuwa suna jiran Shari a.
Kwamishinan CP Aliyu Adamu ya kara da cewa rundunan tayi nasarori da dama da suka hada kwato kayaki harma da tarwatsa masu tada zaune tsaye daga maboyarsu da dai sauransu.
Rundunan tayi kuma nasaran gano makamai da dama da suka hada bindigogi kiran Ak 47 guda ashirin da arbarshe dari shida dama sauran makamai.
Da wannan ne kwamishinan yake kira ga al umma da su kasance masu baiwa jami an tsaro hadin kai da goyon baya domin ganin hukumomin tsaro su cimma burinsu na samar da tsaro da kuma kare rayuka da dukiyoyin Al umma baki daya.
