Za A Farfado Da Ayyukan ‘Yan Sa Kai A Zamfara – Matawalle

Rahotanni daga Jihar Zamfara na bayyana cewar Gwamnatin jihar za ta farfado da kungiyar hadin guiwa ta tsaro na farar hula ta CJTF wacce aka fi sani da “Yan sa kai” don kawo tallafi ga jami’an tsaron jihar akan ‘yan ta’addan da suka addabi Zamfara.

Shugaban kwamitin tsaro da yanke hukunci ga ‘yan bindiga na jihar Zamfara, Abdullahi Shinkafi, ya bayyana hakan a wata tattaunawa da kamfanin dillacin labarai NAN yayi da shi a ranar Talata.

Gwamnatin jihar ta yanke shawarar ne don kawo karshen duk wasu ‘yan ta’adda da ke jihar da dawo da natsuwa ga jama’ar jihar. Shinkafi, wanda shi ne mai bai wa gwamna Bello Matawalle shawarwari a harkar gwamnati ne ya ce: “Gwamnatin jihar ta yanke wannan shawarar ne bisa ganin yadda ayyukan ta’addanci da garkuwa da mutane suke ci gaba da yawaita a fadin jihar.

“Gwamnatin za ta yi hakan bisa wani sabon sharadi. Wajibi ne duk mai neman shiga kungiyar ‘Yan sa kai’ zai gabatar da mutane 3 su kasance tsayayyu a gare shi kafin a jaddada shi.” “Za a farfado da rundunar Yansakai don taimako ga jami’an tsaro wurin ganin karshen duk wasu ‘yan bindiga da masu basu bayanai.”

Related posts

Leave a Comment