Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Sokoto na bayyana cewar wasu gungun Yan bindiga sun kai sabon hari wani ?auye a ?aramar hukumar Tangaza, jihar Sokoto, inda suka hallaka mutum shida, da raunata wasu da dama.
Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun farmaki ?auyen, wanda mafi yawancin mutanen cikinsa mafarauta ne, da sanyin safiyar ranar Lahadi. Kuma yan bindigan sun kai harin ne dai-dai lokacin da mafi yawan mazan garin sun fita sana’arsu ta farauta.
Sai dai babu tabbacin cewa ko harin miyagun yana da ala?a da kashe yan bindiga 13 da mutane suka yi, wa?anda suka kai hari garin Tangaza ranar Asabar.
Wata majiya ta shaidawa Dailytrust cewa wasu mata biyu na cikin wa?anda miyagun maharan suka hallaka a lokacin harin. Yace: “Sun bindige mata guda biyu har Lahira, yayin da suka yanka matasa guda hu?u yayin mummunan harin.”
“Dukka yan bijilanti da kuma yan sa kai dake yankin sun bazama cikin daji domin neman wa?anda suka aikata wannan mummunan ta’addancin.”
A ranar Asabar, fusatattun mutane suka she?e tare da ?one gawarwakin wasu yan bindiga 13, wa?anda suka kai hari garin Tangaza suka kashe mutum hu?u.
