Rahotanni daga Lokoja babban birnin Jihar Kogi na bayyana cewar Wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton ‘yan fashin daji ne sun kai hari kan wani coci a jihar Kogi, inda suka kashe mutum daya tare da yin garkuwa da wasu masu ibada guda uku.
Lamarin ya faru ne da safiyar Lahadi a Cocin ECWA da ke Okedayo na garin Kabba, hedkwatar karamar Hukumar Kabba Bunu ta Jihar Kogi. Lamarin ya faru duk da cewa Gwamna Yahaya Bello ya bayyana jihar a matsayin mafi aminci a Najeriya.
READ ALSO ‘Yan bindiga sun tare motar ‘yan sanda sun kashe jami’ai, sun bakawa motarsu wuta Yahaya Bello, Gwamnan jihar Kogi | Hoto: premiumtimesng.com
Harin ya faru ne kwanaki bakwai kacal bayan da aka kai hari cibiyar kula da gyaran hali ta tarayya da ke Kabba; da kuma sace wasu manoman kaji guda uku a gonarsu.
An ce masu garkuwar sun kai hari cocin ne yayin da ake gudanar da hidimar ranar Lahadi. Cocin yana kusa da babban titin Kabba-Okene.
Lokacin da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kogi, DSP William Aya, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya kara da cewa jami’an su na bin sawun wadanda ake zargin.
