Rundunar sojin Najeriya ta ce ta ceto Manjo Datong, sojan da ?an bindiga suka sace a harin da suka kai kwalejin koyon aikin soja ta NDA a Kaduna a watan da ya gabata.
Cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar a ranar Juma’a ta ce an ceto sojan ne bayan musayar wuta da ?an bindiga tare da tarwatsa sansaninsu da suke tsare da jami’in sojan a yankin Afaka- Birnin Gwari.
Sanarwar ta kuma ce ?an bindiga da dama ne aka kashe a farmakin da sojojin suka kai tare da taimakon ?an sanda a ranar Juma’a.
“Sojojin sun yi nasarar ceto jami’in sojan, ko da yake ya samu rauni amma an yi masa magani,” in ji sanarwar.
A ranar 24 ga watan Agusta ne ?an bindiga suka abka makarantar sojoji ta NDA da ke Kaduna inda suka kashe sojoji biyu kuma suka sace ?aya.
Harin dai ya girgiza ?an Najeriya, kasancewar yadda ?an fashin masu satar mutane da suka addabi arewa maso yammacin Najeriya har suka shiga makarantar inda ba a ta?a zato za su iya abka wa.
