Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya tsinewa ?an bindiga da masu ?aukar nauyin su a ?asar nan. Wa?annan na daga cikin kalaman gwamna El-Rufai a lokacin da yake jawabi ga ?an jihar a tattaunawa da yayi da tashoshin radiyo na jihar a fadar gwamnatin jihar ranar Talata. El-Rufai ya ce za a toshe layukan sadarwar wasu kananan hukumomi da ?an bindiga suka tsananta kai hare-hare da zarar jami’an tsaro sun bu?aci a yi haka. Bayan kammala wannan tattaunawa da yayi da jawabi ga ?an jihar ranar Talata, kwamishinan tsaron jihar…
Read MoreCategory: Tsaro
Tsaro
Mun Kammala Shirin Toshe Layukan Sadarwa A Kaduna- El Rufa’i
Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya ce ya riga ya nemi izinin Gwamnatin Tarayya kan rufe layukan sandarwar kuma ya samu amincewar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari. “Ina so mutanen Jihar Kaduna su sani cewa ko gobe (Laraba) sojoji suka ba mu tabbaci za mu iya rufe layin sadarwa,” inji shi. A hirarsa da gidajen rediyon jihar ranar Talata da dare, gwamnan ya ce, “Babu shakka ’yan bindiga da sauran masu aikata manyan laifuka sun dogara ne da hanyar sadarwa wurin yin magana da masu basu bayanai da kuma dangin wadanda…
Read MoreAbuja: An Harbe ‘Yan Shi’a 8 Masu Zanga-Zanga
Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Kungiyar ‘yan shi’a mabiya Zakzaky ta yi zargin cewa an kashe mabiyanta lokacin da ‘yan sanda suka tarwatsa jerin gwanon zanga-zangar da suke yi na ranar arba’in a ranar Talata a Abuja Haka kuma kungiyar ta ce an jikkata mabiyanta da dama sannan wasu da yawa ba a san inda suke ba. Sai dai ‘yan sanda sun ce babu wanda ya rasa ransa a hargitsin. Daruruwan mabiya shi’a sun yi zargin cewa ‘yan sanda sun auka musu a yayin da suke gudanar…
Read MoreFilato: An Gurfanar Da Wadanda Suka Kashe Matafiya Gaban Kotu
Rahotanni daga Jihar Filato na bayyana cewar Rundunar ‘yan sanda na jihar sun gurfanar da wasu mutane 10 da ake zargin su da hannu a kashe wasu Fulani da tafiya ta bi da su ta Jos a ‘yan watannin baya. Rahotanni sun tabbatar da cewar an hallaka wadannan mutane ne yayin da suka bi ta titin Gada-biyu zuwa Rukuba, garin Jos, a jihar Filato a cikin tsakiyar watan Agusta. Jami’an tsaron sun gurfanar da wadanda ake zargi da wannan laifi a babban kotun jiha da ke Filato. Lauyar da ta…
Read MoreGwamnatin Kaduna Ta Tabbatar Da Kisan Mutum 34 A Kudancin Jihar
Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Gwamnatin jihar ta tabbatar labarin kisan mutane talatin da hudu da yan bindiga sukayi a karamar hukumar Kaura ta jihar Kaduna ranar Lahadi. Mun kawo muku cewa wasu batagari sun kona gidaje a kauyukan Madamai da Abun dake karamar hukumar Kaura a jihar Kaduna. Kwamishanan tsaro da lamuran cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya saki jawabi ranar Litinin, 27 ga Satumba, 2021. A cewarsa, kawo yanzu mutum 34 aka tabbatar da an kashe yayinda Sojoji suka kashe wutar da aka cinnawa…
Read MoreTsaro: Babu Shugabanci A Najeriya – Sule Lamido
Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Alhaji Sule Lamido, tsohon gwamnan jihar Jigawa ya ce Nijeriya ba ta da shugabancin da ake bukata domin tunkarar kalubalen rashin tsaro a kasar. A yayin da ake zantawa da shi a shirin ‘Sunday Politics’ a gidan talabijin na Channels, a ranar Lahadi, Lamido ya ce ya zama dole gwamnati ta rika fadawa mutane gaskiya kan halin matsalar tsaro da kasar ta tsinci kan ta a ciki. “Ya kamata mutane su rika bibiyar gwamnati kan alkawurran da ta yi kuma bana son…
Read More‘Yan Bindiga Sun Hallaka Mutane 30 A Kudancin Kaduna
A?alla mutum 30 suka mutu sannan an kona gidaje da dama a kauyukan Madamai da Abun na karamar hukumar Kaura da ke jihar Kaduna. Jaridar Daily Trust ta rawaito tsohon shugaban kungiyar hadin-kan matasan Kaura, Kwamared Derek Christopher na cewa maharan sun kutsa yankunan da misali karfe 5 na yamma suka rinka harbe-harbe kan mai uwa dawabi. Ya kuma shaida cewa yawancin mutanen da aka jikkata an kai su asibiti domin basu kulawa. Rundunar ‘yan sanda Kaduna kawo yanzu ba ta ce komai a kan harin ba.
Read MoreDa Dumi-Dumi: Gwamnonin Arewa Na Taron Gaggawa A Kaduna
Gwamnonin arewacin Najeriya na taron gaggawa a yau Litinin a Kaduna domin tattauna batutuwan da suka danganci harajin VAT. Rahotanni na cewa gwamnan Kaduna, Mallam Nasiru El-Rufai ne zai karbi bankwancin taron wanda shugaban kungiyar gwamnonin arewa kuma gwamnan Filato, Simon Lalong zai jagoranta. Taron na zuwa ne bayan ministan shari’a a Najeriya, Abubakar Malami ya shaida cewa babu wata jiha da ke da ikon karbar harajin kasa. Batun bai wa jihohin damar karban harajinsu kamar yadda wasu jihohin kudu da suka hada da Legas da Rivers ke ta fafutika…
Read MoreKungiyar OPC Ta Yi Tir Da Ziyarar Gumi Kasar Yarbawa
Kungiyar Yarabawa ta Oodua Peoples Congress, OPC, reshen jihar Oyo karkashin jagorancin Aare Onakakanfo na kasar Yarbawa, Gani Adams ta ce ziyarar da Gumi ya kai ta bazata jihar Oyo cin fuska ne ga Yarbawa baki daya. A yayin zantawarsa da manema labarai a karshen mako, Rotimi Olumo, jagorar OPC a jihar Oyo ya ce Gumi yana wuce gona da iri kuma ya gargade shi ya kiyayi yankin Kudu maso Yamma na kasar Yarbawa. A cewar Olumo, ziyarar Gumi babban barazana ce ta tsaro ga dukkan yankin Yarbawa domi ba…
Read MoreSokoto: ‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Barikin Sojoji
Rahotanni daga Jihar Sokoto na bayyana cewar wasu Tsagerun yan bindiga sun kai hari sansanin sojoji a ?aramar hukumar Sabon Gari, jihar Sokoto, inda suka kashe jami’ai da dama. Wakilin Dailytrust ya gano cewa barikin sojojin dake a Kauyen Dama, an la?aba masa suna, “Sansanin Burkusuma.” Wata majiya ta bayyana cewa maharan sun kai hari sansanin sojojin ne da sanyin safiyar ranar Jumu’a da ta gabata. Tsohon shugaban karamar hukumar Sabon Gari, Idris Muhammad Gobir, ya shaidawa wani mutumi mai suna ?ancha?i, wanda ya tabbatar da kai harin. Mutumin ya…
Read MoreAdamawa: An Yi Nasarar Cafke Mutanen Dake Addabar Yola Da Fashi
Rundunan yan sandan jahar Adamawa tayi nasaran kama mutane uku da ake zargi da yin fashi wajen shiga gidajen al umma a cikin karamar hukumar yola ta kudu dake jahar Adamawa. Rundunan ta baiyana haka ne a wata sanarwa dauke da sanya hanun kakakin rundunan D S P Suleiman Yahaya Nguroje, wanda aka rabawa manema labarai a yola. Sanarwan ya cigaba da cewa an samu nasaran kama mutanen ne biyo bayan bayanain sirri da suka samu daga mazauna garin na yola dangane da ahiga gidaje da mutanen keyi da da…
Read MoreKatsina: Mata Mafarauta Sun Sha Alwashin Ganin Bayan ‘Yan Bindiga
Rahotanni daga Jihar Katsina na bayyana cewar Kungiyar mafarautan Najeriya, NHC, reshen jihar Katsina da ke arewa maso yamma ta yanke shawarar taimaka wa gwamnatin jihar yaki da ta’addanci a fadin jihar. Hajiya Ummah Dauda, mataimakiyar kwamanda janar na kungiyar, ta jagoranci sauran ‘yan kungiyar zuwa ofishin sakataren gwamnatin jihar, Mustapha Muhammad Inuwa, inda ta bada wannan tabbaci. Yayin jawabi a ofishin Sakataren Gwamnatin Ummah ta bayyana cewa a cikin kungiyar mafarautan za su iya sadaukar da ran su wurin kawo karshen ta’addanci a jihar. Kamar yadda ta ce: “A…
Read MoreBauchi: Jama’ar Birshin Fulani Za Su Yi Barci Da Minshari – Kakakin ‘Yan Sanda
Rundunar Yan’sandan Jihar Bauchi ta tashi haikan wajen dakile ayyukan yan’tadda da masu garkuwa da mutane a yankin Unguwar Birshin Fulani da kewayen ta da ma sauran al’umman a sassbanbance titin hanya Bauchi zuwa Dass a yan’ kwanakin da suka wuce Yace yanzu haka sun tsaurar matakan tsaro a yankin ta wajen samar da motoci masu sulke da zirga zirga na awa ashirin da hudu 24, tare da hadin gwiwa da sauran Jami’an tsaro da mutanen gari, kai sumame a kowani lokaci, lungu da sako na yankin kana da sa’ido…
Read MoreKaduna: An Yi Nasarar Damke Maharan Makarantar Bethel Baptist
Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Rundunar ‘Yan sanda sun cafke masu garkuwa da mutane uku da ke da hannu a sace dalibai sama da 100 na makarantar Bethel Baptist, dake Jihar Kaduna. An rawaito cewa jami’in hulda da jama’a na rundunar, Frank Mba ne ya gabatar da wadanda ake zargin, wadanda ke sanye da kayan sojoji, a hedikwatar runduna ta musamman da ke yaki da fashi da makami (SARS), a Abuja. An tattaro cewa wadanda ake zargin, Adamu Bello, Isiaku Lawal da Muazu Abubakar, sun shaidawa manema…
Read MoreZa Mu Karbi Tubabbun Boko Haram Hannu Biyu-Biyu – Shehun Borno
Rahotanni daga Maiduguri babban birnin Jihar Borno na bayyana cewar mai Martaba Shehun Borno, Alhaji Abubakar Ibn Umar Garbai Al-Amin El-Kanemi a ranar Laraba ya ce ana ta kokarin ganin an kammala shirin mayar da tubabbun mayakan Boko Haram cikin jama’a don samar da zaman lafiya mai dorewa cikin al’umma. An ruwaito cewar Shugaban Majalisar Sarakunan gargajiyan ya yi maganar ne a wani taro na kamfen din wayar da kai wurin kokarin mayar da tubabbun mayakan cikin jihar Borno. A cewar sa ta’addanci a jihar ya dauki lokaci mai tsawo…
Read MoreObasanjo Ya Karbi Kwangilar Kawo Zaman Lafiya A Afirka
Rahotannin dake shigo mana yanzu na bayyana cewar Shugaban kungiyar kasashen Afrika ta AU, ya hada Olusegun Obasanjo da aikin kawo zaman lafiya a cikin fa?in nahiyar Afirka gaba ?aya. An ruwaito cewa tsohon shugaban kasar Najeriya zai yi kokarin tabbatar da zaman lafiya, kwanciyar hankali da lumana a gabashin Afrika. Olusegun Obasanjo ya isa birnin Addis Ababa ta kasar Habasha domin fara aikin da aka ba shi na babban jakadan kungiyar AU a kasashen da ke yankin. Ana sa rai Obasanjo wanda yana cikin dattawan Afrika ya kawo karshen…
Read MoreHallaka ‘Yan Bindiga Ne Mafita Ga Matsalar Tsaro – Sarkin Katsina
Rahotanni daga birnin Katsina na bayyana cewar Mai martaba Sarkin Katsina ya ce tunda ?an bindiga sun za?i su rika kashe mutane ‘suma bai dace a bar su da rai ba’. Sarkin na Katsina, Abdulmuminu Usman ya ce ba abin da ya dace da ?an bindigan da ke kashe mutane a arewa maso yamma illa kisa. Sarkin ya yi wannan furucin ne yayin taron tsaro na masu ruwa da tsaki a ranar Talata a Katsina kamar yadda Premium Times ta ruwaito. Wadanda suka hallarci taron sun hada da Gwamna Aminu…
Read More‘Yan Bindigar Zamfara Sun Fara Kaura Zuwa Kano – Dan Majalisa
Rahotanni da muke samu yanzu na bayyana cewar hare-haren da sojoji suke kai wa ’yan bindiga a jihohin Katsina da Zamfara sun tilasta musu tserewa zuwa Jihar Kano da ma wasu jihohin. Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Rogo da Karaye a Majaliar Wakilai, Haruna Isah Dederi, ya ce a kwanakin baya ’yan bindiga sun kai hare-hare gami da garkuwa da mutane a garuruwa bakwai a Karamar Hukumar Rogo ta Jihar Kano. Ya ce garuruwan da ’yan bindiga suka yi garkuwa da mutane a yankin sun hada da garin Jajaye, Zarewa,…
Read MoreTsaro: Ya Kamata A Cusa Matasa Aikin Soja – Abdulwahid
An Bukaci Matasan Nijeriya Su Kara Yin Karatun Ta-Natsu Don Kaucewa Fadawa Munanan Hali Musamman a Wannan Lokaci da Muke ciki. Wannan Kira Ya Fitone Daga Bakin Wani Matashi Mai Suna Abdulwahid Umar Haza A lokacin Da Yake ganawa Da Manema Labarai a Kaduna. Binhaz ya ce Halin da Matasa Suka Tsunduma Kansu Na Shaye-Shaye ne Ya Kara Jefa Matasan Cikin Halin Kaka ni Kayi, Inda ya Kara da cewa Akwai Bukatar Matasan Su Rungumi Wata Sana’a Domin Su Dogara Da Kansu Basai Sun Jira Gwamnati ba. Daga Karshe Abdulwahid…
Read MoreKarkashe ‘Yan Bindiga Ne Mafita Ga Matsalar Tsaro – Sarkin Katsina
Rahotanni daga Jihar Katsina na bayyana cewar Mai martaba Sarkin Katsina, Abdulmuminu Usman, ya ce babu abin da ‘yan bindiga da ke kashe mutane a arewa maso yamma suka cancanta face mutuwa. Sarkin na magana ne yayin taron masu ruwa da tsaki kan harkar tsaro a ranar Talata a Katsina. Wadanda suka halarci taron sun hada da Gwamna Aminu Masari, Ministan Yada Labarai da Al’adu, Lai Mohammed, Sarkin Daura, Umar Faruk Umar, da wasu da dama. Sarkin ya ce tunda ‘yan fashin sun yanke shawarar daukar rayukan mutane, su ma…
Read More