Yobe: Mutane Da Dama Sun Mutu Dalilin Aman Wutan Jiragen Yaki

Wani jirgin yaki ba a tantance daga ina yake ba ya yi aman wuta a yankin kauyen Buhari da ke karamar Yunusari a jihar Yobe da safiyar Laraba, inda ya yi sanadin mutuwar fararen hula da dama.

Al’ummar garin sun ce shaida wa BBC cewa sun wayi gari ne da ganin jiragen yaki har uku suna shawagi a sararin samaniyar garin nasu.

Daga bisani daya daga cikin jiragen ya yi aman wuta kan wani bangaren garin, kamar yadda wani da ‘yan uwansa suka mutu a lamarin ya shaida wa BBC.

“Da safe kamar karfe 8.30 ne abin ya faru, har zuwa lokacin da daya daga cikin jiragen ya fado wani bangaren na garin yana ta zubar da wuta, duk gidajen da ke wannan bangaren sai da suka lalace.

“Jirgin babba ne sosai irin na sojoji, amma ba mu san na ina ne ba,” in ji shi.

Ganau din ya ce ba za su iya sanin adadin mutanen da suka rasu ba zuwa yanzu, “don ko a cikin gidanmu ma mun rasa mutum biyu,” in ji shi.

Ya ce cikin mamatan gidansu akwai matar babansa da ‘yar yayarsa, “amma ni ba na gida lokacin muna gefen gari a kan idonmu komai ya faru.

Sai dai ya ce har yanzu babu jami’in tsaron da ya je wajen, “don da akwai yaran Boko Haram da ke shawagi sosai a yankin.”

Ganau din ya ce su ‘yan gari ya su-ya su ne suka yi aikin kwasar gawarwaki da wadanda suka jikkata zuwa asibitn garin Geidam, saboda rashin kyawun sadarwa ma ba zai sa su tsaya bata lokacin yin waya ba, kamaar yadda ya ce.

Related posts

Leave a Comment