Rahotanni daga Maiduguri babban birnin Jihar Borno na bayyana cewar wani tsohon kwamandan ‘yan ta’addan Boko Haram, Adamu Rugurugu, ya ce ya yi watsi da ta’addanci ne sakamakon gano cewa akidar ‘yan ta’addan Boko Haram zamba ce.
A cikin bidiyon da PRNigeria ta samu, kasurgumin dan ta’addan ya ce manyan shugabannin kungiyar a koyaushe za su aika su a kashe su ne a fagen daga, tare da yaudarar su cewa aljanna ce za ta zama makomar su idan an kashe su.
A cewar Rugurugu, manyan shugabannin Boko Haram ba sa iya tunkarar sojoji sai dai buya daga baya suna amfani da mayakansu wajen kai hare-haren kan sojoji a arewa maso gabas.
Malam Rugurugu ya kuma yi wa sojojin Najeriya addu’ar nasara, tare da hada wa da la’antar wadanda ba sa son zaman lafiya a Najeriya.
