Ba Za A Taba Halasta Tabar Wiwi A Najeriya Ba – Marwa

Shugaban Hukumar Hana sha da Fataucin miyagun ?wayoyi na ?asa NDLEA Birgediya-Janar Buba Marwa mai ritaya, ya bayyana dalilan daya sa gwamnati bazata ta?a halasta shan wiwi a Nigeria. Marwa yayi jawabi a wani taron lakca da Ulefunta na shekarar 2021, wanda ?ungiyar Deji ta Masarautar Akure a jahar Ondo ta shirya. Taron Oba Aladetoyinbo Aladelusi da tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya Chief Olu Falae suka jagoran ta.Buba Marwa Wannan na ?unshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan kafafen ya?a labaru Femi Babafemi ya fitar, yace Marwa ya samu wakilcin Mai bashi…

Read More

Zamfara: Yunwa Ta Tursasa Wadanda Aka Yi Garkuwa Dasu Cin Ciyawa

Rahotanni daga Jihar Zamfara na bayyana cewar wasu daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su a sassa daban-daban na jihar Zamfara sun koma cin ciyawa domin kada su mutu a yayin da wadanda suka sace su suka rasa abincin ba su. Daya daga cikin wanda abin ya faru da su wacce ta ce sunanta Iklima Murtala, ta yi ikirarin cewa mutane 17 sun mutu saboda tsananin yunwa, a dokar daji a hannun ‘yan Bindiga. Da ya ke karbar wadanda aka ceto a madadin gwamnati, sakataren gwamnatin jihar Zamfara, Alhaji…

Read More

Matsalar Tsaro: El Rufa’i Ya Bar Jaki Ya Koma Dukan Taiki – Mai Rakumi

An bayyana matakan da gwamnatin Jihar Kaduna ?arkashin jagorancin Gwamna Nasiru El Rufa’i ta dauka na haramta hawa Babura da cin kasuwanni da sunan magance matsalar tsaro, a matsayin wani aiki da aka bar Jaki aka koma dukan taiki. Bayanin hakan ya fito ne daga bakin wani jigo a siyasar Jihar Kaduna Alhaji Umar Ibrahim Mai Ra?umi, a yayin wata tattaunawa da yayi da manema labarai a Kaduna dangane da halin kunci da jama’ar Kaduna ke ciki tun bayan haramta hawa Babura a Jihar. Mai Ra?umi wanda ya bada shawarar…

Read More

Babu Wani Shiri Na Sake Dawo Da SARS – Baturen ‘Yan Sanda

Sufeto Janar na ‘yan sanda Najeriya Mista Usman Baba, ya tabbatar wa da ‘yan Najeriya cewa babu wani shiri na mayar da runduna ta musamman data ruguje mai yaki da fashi da makami cikin rundunar ‘yan sandan Najeriya. Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan Sanda Mista Frank Mba, shine wanda ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa, ranar Alhamis, a Abuja. Mba yace karin haske ya biyo bayan rahotannin da ke zaga yawa a kafofin sadarwa da kuma inda ba kafofin sadarwa ba cewa IGP ya bada umarnin sake…

Read More

Sokoto: Gwamna Tambuwal Ya Haramta Ayyukan ‘Yan Sa Kai

Rahotanni daga Jihar Sokoto na bayyana cewar wasu yan bindiga da ake tsammanin yan ?ungiyar sakai ne da aka haramta, sun hallaka mutum 11 a a kauyen Jihar Sokoto. Rahotanni sun bayyana cewa akwai limamin masallaci daga cikin mutanen da maharan suka kashe a ?auyen Mamande, ?aramar hukumae Gwadabawa. An ruwaito cewa baki ?aya mutanen sun mutu ne nan take, yayin da wasu mutum hu?u da suka jikkata aka kaisu asibiti domin duba lafiya. Limamin da lamarin ya shafa, Malam Aliyu, an tabbatar da cewa shine yake jagorantar musulmai sallah…

Read More

Majalisar Addinai Ta Yi Kiran Kama Wadanda Suka Kashe Fasto A Kano

Rahotanni daga Jihar Kano na bayyana cewar Shugaban Majalisar koli ta harkokin addinin Musulunci Mai alfarma Sarkin Musulmi Dr Sa’adu Abubakar lll, da Shugaban kungiyar kiristocin Nigeria, CAN, Ayokunle sun bukaci ‘yan sanda su kama wasu batagari musulmai bisa halaka wani Fasto da su ka yi a Kano. Rahotanni sun bayyana cewar sai da suka babbaka gidan faston, cocin da yake wa’azi da makarantar da yake kula da ita, kafin suka Hallaka shi. A wata takarda wacce sakataren kungiyar, Cornelius Omonokhua ya sa hannu, ya nuna alhininsa akan kisan faston…

Read More

Zamfara: An Kubutar Da Mutane Masu Yawa Daga Hannun ‘Yan Bindiga

Rahotanni daga birnin Gusau fadar Jihar Zamfara na bayyana cewar Gwamnatin jihar a ranar Alhamis ta ce ta tabbatar da sakin akalla mutane 200 da ‘yan bindiga suka sace ta hanyar tattaunawa ta lumana da sauran matakan tsaro. Mukaddashin Gwamnan Zamfara, Nasiru Magarya, ya bayyana hakan lokacin da ya karbi bakuncin Taron Shugabannin Majalisar Dokokin Jihohin Najeriya, a Gusau. Alhaji Magarya, wanda shine kakakin majalisar dokokin Zamfara, ya tarbi tawagar, wacce ta kai masa ziyarar jaje bisa rasuwar mahaifinsa, Mu’azu Magarya. A baya mun kawo muku rahoton cewa, Mahaifin Kakakin…

Read More

Kaduna: Rikicin Cikin Gida Ya Hallaka ‘Yan Bindiga Da Dama

Rahotanni dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar akalla ‘yan ta’adda 30 aka kashe bayan arangama tsakanin kungiyar’ yan ta’adda ta Ansaru da ‘yan fashi a kewayen Damari na karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna. A cewar rahoton Daily Trust, majiyoyi da yawa sun tabbatar da cewa kungiyoyin masu aikata laifuka guda biyu sun fara fafutukar neman matsayi a makon da ya gabata. Wannan na zuwa ne makwanni uku bayan rufe hanyoyin sadarwa a jihar Zamfara, lamarin da ya tilastawa ‘yan ta’adda tserewa zuwa kauyukan Saulawa da…

Read More

Da Yiwuwar Mu Kakaba Dokar Ta Baci A Jihar Anambra – Ministan Shari’a

Rahotanni daga fadar Shugaban kasa dake babban birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnatin tarayyar ta ce za ta iya saka dokar ta-?aci a Jihar Anambra da ke kudancin ?asar domin tsaurara tsaro yayin gudanar da za?en gwamna a watan Nuwamba. Ministan Shari’a Abubakar Malami ne ya bayyana hakan jim ka?an bayan kammala taron Majalisar Zartarwa ranar Laraba wanda Shugaba Buhari ya jagoranta. Malami ya ce gwamnati za ta yi dukkan mai yiwuwa domin ta tabbatar da tsaron lafiyar mutane da dukiyoyinsu “idan gwamnatin jihar ta gaza yin hakan”. “Idan…

Read More

Da Dumi-Dumi: An Damke Direban Dake Kai Wa ‘Yan Bindiga Fasinjoji

Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja ta yi holan Hamisu Sule wani direba dake daukar fasinja yana tsayawa da su a daidai wajen da ‘yan bindiga suke fitowa domin suyi garkuwa da mutane. A cewar kakakin rundunar’yan sandan babban birnin tarayya Abuja Frank Mba, shi wannan direba, bakinsa daya da ‘yan bindigar dake sace mutane suna yin garkuwa da su, idan ya dauko mutane sai yazo wajen da ya san ‘yan bindigar na labe sai ya nuna mota ta samu matsala. Daga bisani kuma sai ‘yan bindiga su fito…

Read More

Ba Ni Bane A Bidiyo Dauke Da Bindiga- Ministan Tsaro

Wata sanarwa da mai taimaka wa ministan kan kafofin sada zumunta Mohammad Abdulkadri ya fitar ta ce masu son ta da zaune tsaye ne ke yada hoton da sunan Janar Magashi. Ta kuma ce bincike ya gano cewa mutumin da ke cikin bidiyon shugaban kwalejin rundunar sojin Najeriya na kimiyya da fasaha da ke Makur?i wato Nigerian Army College of Environmental Science and Technology (NACEST) Makurdi, wanda mu?aminsa ya ba shi damar ri?e makamai idan zai yi tafiya. Sanarwar ta zayyano wasu abubuwa kamar kalar motar da mutumin ya shiga…

Read More

Mai Daukar Hotunan Boko Haram Ya Mika Wuya

Rahotanni daga birnin Maiduguri fadar gwamnatin jihar Borno na bayyana cewar Wani mai daukar hoton bidiyo da ke aiki tare da kungiyar ta’addanci, Boko Haram, ya mika kansa ga jami’an gwamnati a jihar Borno da ke a Arewa maso gabashin Najeriya. Mai daukar hoton bidiyon wanda har yanzu ba a bayyana sunansa ba, a halin yanzu yana tsare a wani gidan gwamnati tare da daruruwan sauran ‘yan ta’adda da suka mika wuya, HumAngle ta ruwaito. Babban jami’in gwamnatin jihar Borno ya ce: “Yanzu muna da daya daga cikin manyan masu…

Read More

Zamfara: Mahaifin Shugaban Majalisa Ya Mutu A Hannun ‘Yan Bindiga

Rahotannin dake shigo mana daga Birnin Gusau babban birnin Jihar Zamfara na bayyana cewar Alhaji Abubakar, mahaifin kakakin majalisar dokokin jihar Zamfara, Hon. Nasiru Magarya ya mutu yayin da yake a tsare hannu masu garkuwa da mutane. Mahaifin Kakakin wanda shine Hakimin kauyen Magarya, yan bindiga sun yi garkuwa da shi makwanni takwas da suka gabata, tare da matarsa, da kuma jariri dan makonni uku da haihuwa. Yayin da aka ceto wadanda aka sace a jiya Asabar, mahaifin kakakin Majalissar baya cikin su. Kazalika da yake jawabi ga manema labarai,…

Read More

Sokoto: ‘Yan Bindiga Sun Sake Sabon Salo

Rahotanni daga Jihar Sokoto na bayyana cewar ‘yan Bindiga sun fitar da wani sabon salo a jihar inda yan bindigan suka aikawa Dagacin Burkusuuma a karamar hukumar Sabon Birni da wata zungureriyar wasika ta neman kudin fansa. A cikin wasikar, yan bindigan sun bukaci Dagacin ya nemi kudi daga wajen iyalan wadanda suka sace da abokansu na arziki. A wasikar dake dauke sunayen mutum 19, yan bindigan sun bukaci daya daga cikin wadanda suka sace ya bayyana halin da suka ciki. A wasikar an bayyana sunayen wadanda aka sace da…

Read More

Ba A Yi Kuskure Ba Wajen Hallaka Masunta A Borno – Hukumar Tsaro

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Hedikwatar tsaro ta Najeriya tayi karin haske game da kashe wasu masunta 20 da sojoji suka yi a jihar Borno a makon da ya gabata. Hedikwatar tsaro na kasar watau DHQ tace ta hallaka ‘yan ta’addan ISWAP ne da suka fake da kamun kifi, suna yin ta’adi a yankin tafkin Chadi. A wani jawabi da hedikwatar ta fitar ta bakin darektan harkokin yada labarai, Birgediya-Janar Benard Onyeuko, ta bayyana ainihin abin da ya faru. Birgediya-Janar Benard Onyeuko yace sojoji sun gano ‘yan…

Read More

‘Yan Jarida Sun Fi ‘Yan Bindiga Ta’addanci – Gumi

Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Sanannen Malamin addinin Musulunci Sheikh Ahmad Gumi, ya ce ‘yan jaridar da suke kiran ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda ne asalin ‘yan ta’addan. Kamar yadda Arise News ta ruwaito, ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da gidan Talabijin din Arise ta yi da shi, ya ce akwai bu?atar a rungumi ‘yan bindiga a al’umma. Daya daga cikin mai gabatar da shirin ya bayyana yadda hatsarin ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda suke yayin da ya tambayi malamin abinda suke so kafin su zubar…

Read More

An Sake Bude Layukan Sadarwa A Zamfara

Rahotanni daga Gusau babban birnin Zamfara na bayyana cewarGamnatin jihar ?arkashin jagorancin Gwamna Bello Matawalle ta sanar da bude layukan sadarwa a Gusau babban birnin Jihar. Kwamishinan yada labarai na Jihar Ibrahim Dosara ne ya tabbatar wa da BBC hakan. Dosara ya ce baya ga bude layukan wasa an kuma bude kasuwar gusau wadda ita ma a baya aka sanar da rufe ta. “An sauya dokar takaita zirga-zirga ababan hawa daga 8 na yamma zuwa 6 na safe a baya, zuwa 6 na safe zuwa 12 na dare”. A iya…

Read More

Jahilci Ne Ya Sa ‘Yan Ta’adda Ke Kisa – Dr. Gumi

Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Fitaccen malamin addinin Islama mazaunin jihar, Sheikh Dr Ahmad Gumi, ya ce jini mai matukar yawa ne ke kwaranya a Najeriya a kowace rana babu kakkautawa. A yayin jawabi a wani taron tabbatar da zaman lafiya wanda Center For the Advancement of Human Dignity and Value (CAHDV) ta shirya a Kaduna a ranar Alhamis, malamin ya ce ya na mamakin yadda ba a dauki mataki kan zubar jinin ba. Malamin ya ?ara da cewar rashin addini, ilimi da kuma wayewar kai a fannin…

Read More

Arewa Maso Yamma Na Cikin Bala’i – Bafarawa

Rahotanni daga Jihar Sokoto na bayyana cewar tsohon gwamnan jihar kuma ?asaitaccen ?an siyasa Alhaji Attahiru Bafarawa ya koka kan yadda mutanen yankin suka noma gonakinsu amma ba za su iya zuwa su girbe amfani ba saboda barazanar tsaro. Alhaji Attahiru Bafarawa, ya ce kamata ya yi Gwamna Bello Matawalle, ya zagaya sassan jiharsa ta Zamfara don tantance tasirin matakan da ya ?auka na kassara ‘yan fashin daji da kuma ?ullo da matakan rage ra?a?i ga jama’a. Tsohon gwamnan ya kuma bu?aci Shugaba Muhammadu Buhari, da shi ma ya kai…

Read More

Ranar ‘Yancin Kai: Mun Shirya Tsaf A Jihar Adamawa – Rundunar ‘Yan Sanda

Rundunan yan sandan jahar Adamawa tace ta kimtsa tsaf domin daukan dukkanin matakai da suka dace domin ganin angudanar da bkin samun yancin kai cikin lumana ba tare da wata matsalaba. Kwamishinan yan sandan jahar Adamawa CP Muhammed Ahmed Barde ne ya baiyana haka a wata sanarwa dauke da sanya hanun kakakin rundunan D S P Suleiman Yahaya Nguroje wanda aka rabawa manema labarai a yola, Kwamishinan ya umurci dukkanin manyan jami an yan sandan dake fadin jahar da su tabbata sun tura Jami an tsaro a wuraren da za…

Read More