Rahotanni daga Jihar Zamfara na bayyana cewar wasu daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su a sassa daban-daban na jihar Zamfara sun koma cin ciyawa domin kada su mutu a yayin da wadanda suka sace su suka rasa abincin ba su.
Daya daga cikin wanda abin ya faru da su wacce ta ce sunanta Iklima Murtala, ta yi ikirarin cewa mutane 17 sun mutu saboda tsananin yunwa, a dokar daji a hannun ‘yan Bindiga.
Da ya ke karbar wadanda aka ceto a madadin gwamnati, sakataren gwamnatin jihar Zamfara, Alhaji Kabiru Balarabe ya ce: “Gwamnati za ta cigaba da ragargazan ‘yan bindigan har sai sun gaji sun ajiye makamai sun mika wuya.”
Kwamishinan ‘yan sanda a jihar ta Zamfara, Ayuba Elkana, ya ce saboda matsin lambar da rashin abinci, ‘yan bindigan sun tsinci kansu a mawuyacin hali. Ya ce: “A halin yanzu suna matukar shan wahala kuma ba su iya aikata abubuwan da suka saba yi domin mun dakile su.”
Da ya ke magana da manema labarai kakakin gwamnan jihar, Zailani Bappa, wanda ya tabbatar cewa an sako mutum 185 da aka yi garkuwa da su ya ce gwamnati na kulawa da magungunansu.
“Mutane 185 aka ceto. Abin farko da muke yi a Zamfara idan an ceto mutane shine kai su asibiti don duba lafiyarsu. Ana duba su don ganin ko sun kamu da cuta yayin tsare su. Wadanda ke da matsala gwamnati za ta biya kudin maganinsu har su warke kafin a sallame su.
“A kan kuma basu abinci, tufafi da sauran kulawa yayin da suke hannun gwamnati. Bayan sun warke, a kan yi musu gwajin kwakwalwa da magani saboda halin da suka shiga hannun ‘yan bindigan. Idan an musu magani sun warke sai a sada su da iyalansu su cigaba da rayuwa kamar kowa.
