Ba Za A Taba Halasta Tabar Wiwi A Najeriya Ba – Marwa

Shugaban Hukumar Hana sha da Fataucin miyagun ?wayoyi na ?asa NDLEA Birgediya-Janar Buba Marwa mai ritaya, ya bayyana dalilan daya sa gwamnati bazata ta?a halasta shan wiwi a Nigeria.

Marwa yayi jawabi a wani taron lakca da Ulefunta na shekarar 2021, wanda ?ungiyar Deji ta Masarautar Akure a jahar Ondo ta shirya.

Taron Oba Aladetoyinbo Aladelusi da tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya Chief Olu Falae suka jagoran ta.Buba Marwa

Wannan na ?unshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan kafafen ya?a labaru Femi Babafemi ya fitar, yace Marwa ya samu wakilcin Mai bashi shawara na musamman akan magance ?waya Otunba Lanre Ipinmisho.

Sanarwar tace “munga irin ta’addancin daya faru a ?asashe irin su Colombia da Mexico inda aka halasta shan ?waya.

“Akwai manyan abubuwan dake faruwa wanda ba ?ir?ira bane, dagaske ana yin su, yadda miyagun ?wayoyi ke yawan haifar da fa?ace-fadace.

“Abun tambaya a garemu shine: ?waya ta bada gagarumar gudummawa wajen kawo ta?ar?arewar tsaro a Nigeria? Tambaya itace Eh. A dalilin haka muna da dalilin dazai sanya bazamu ta?a halasta shi.

Related posts

Leave a Comment