Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Fitaccen malamin addinin Islama mazaunin jihar, Sheikh Dr Ahmad Gumi, ya ce jini mai matukar yawa ne ke kwaranya a Najeriya a kowace rana babu kakkautawa.
A yayin jawabi a wani taron tabbatar da zaman lafiya wanda Center For the Advancement of Human Dignity and Value (CAHDV) ta shirya a Kaduna a ranar Alhamis, malamin ya ce ya na mamakin yadda ba a dauki mataki kan zubar jinin ba.
Malamin ya ?ara da cewar rashin addini, ilimi da kuma wayewar kai a fannin ‘yan ta’adda shi ne abinda ke kawo hauhawar rashin tsaro a yankin kuma maganin shi shine wayar da kai.
Kamar yadda Gumi ya ce, a shekaru uku da suka gabata, kasar nan ta kashe dala biliyan daya wurin yaki da ‘yan bindiga kuma ya ce ana bukatar wata dala biliyan dayan domin cigaba da yakar hakan, kashi goma kenan daga cikin abinda ake bukata wurin wayar da kan ‘yan bindigan.
“Na gane wani abu daya, rashin addini, rashin ilimi, da jahilci ne abinda ya kawo rashin tsaro kuma maganinsa shi ne a wayar da kai. Idan aka wayar da su, za a iya magance matsalar. Idan ana son shawo kan matsalar kamar yadda aka kirkire ta.
“Abinda mu ke fuskanta a yau shi ake kira da rashin wayewa. Ga jini nan ya na ta kwaranya babu dalili kuma har yanzu ba mu gane darajar dan Adam ba balle amfaninsa. Dan Adam ya na da daraja ba kadan ba, ba a iya tilasta addini a kan kowa. Me yasa jini ke kwaranya a kasar nan?
