Ba Ni Bane A Bidiyo Dauke Da Bindiga- Ministan Tsaro

Wata sanarwa da mai taimaka wa ministan kan kafofin sada zumunta Mohammad Abdulkadri ya fitar ta ce masu son ta da zaune tsaye ne ke yada hoton da sunan Janar Magashi.

Ta kuma ce bincike ya gano cewa mutumin da ke cikin bidiyon shugaban kwalejin rundunar sojin Najeriya na kimiyya da fasaha da ke Makur?i wato Nigerian Army College of Environmental Science and Technology (NACEST) Makurdi, wanda mu?aminsa ya ba shi damar ri?e makamai idan zai yi tafiya.

Sanarwar ta zayyano wasu abubuwa kamar kalar motar da mutumin ya shiga da takardar ke li?e a jikin motar da ya dace a ce masu ya?a bidiyon sun duba kafin su ayyana cewa ministan tsaron ne.

Ta ce ministan na amfani da motar jeep ce ?irar Land Crusier kuma ba?a kamar sauran takwarorinsa ministoci.

Haka kuma, sanarwar ta ce ministan tsaron ba ya bu?atar ya ?auki bindiga saboda kamar yadda aka gani a bidiyon saboda irin tsattsauran tsaron da ke tattare da mu?aminsa.

Ministan ya sanar da cewa al’ummar Najeriya su san cewa ana yin dukkan mai yiwuwa don ganin an da?ile ?an bindiga da masu ta da ?ayar baya a ?asar.

Related posts

Leave a Comment