Da Dumi-Dumi: Buhari Ya Kori Manyan Ministoci Biyu

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaba Muhammadu Buhari ya sauke ministoci biyu na ma’aikatun Noma Sabo Nanono da kuma na Lantarki Sale Mamman.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin shugaban Najeriya, Femi Adesina ya fitar a wannan Larabar.

Sanarwar ta ce Ministan Muhalli, Mohammed Abubakar ne zai maye gurbin Ministan Noma, yayinda karamin Ministan ayyuka, Abubakar Aliyu zai maye gurbin Ministan Lantarki.

Related posts

Leave a Comment