Sokoto: ‘Yan Bindiga Sun Sake Sabon Salo

Rahotanni daga Jihar Sokoto na bayyana cewar ‘yan Bindiga sun fitar da wani sabon salo a jihar inda yan bindigan suka aikawa Dagacin Burkusuuma a karamar hukumar Sabon Birni da wata zungureriyar wasika ta neman kudin fansa.

A cikin wasikar, yan bindigan sun bukaci Dagacin ya nemi kudi daga wajen iyalan wadanda suka sace da abokansu na arziki. A wasikar dake dauke sunayen mutum 19, yan bindigan sun bukaci daya daga cikin wadanda suka sace ya bayyana halin da suka ciki.

A wasikar an bayyana sunayen wadanda aka sace da kuma kudi Naira Miliyan 20 da ake bukatar kudin fansa cikin gaggawa.

Ga jerin sunayensu: Maza 1. Yahaya 2. Bello Sani 3. Maharazu Mamman 4. Naziru Saidu 5. Lawali Nano 6. Abdullahi M Makau 7. Sani Mamman 8. Mustafa Abdullahi 9. Hussaini Ladan Samaila

Mata.. 1. Rashida Abdullahi 2. Rahila Abdullahi 3. Hana M isah 4. Hauwa 5. Maryam Sani 6. Hadiza Labaran 7. Jimma Maidabo Gatawa.

Yara. 1. Safiya A Sani 2. Aisha Labaran

Related posts

Leave a Comment