Kaduna: Rikicin Cikin Gida Ya Hallaka ‘Yan Bindiga Da Dama

Rahotanni dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar akalla ‘yan ta’adda 30 aka kashe bayan arangama tsakanin kungiyar’ yan ta’adda ta Ansaru da ‘yan fashi a kewayen Damari na karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna.

A cewar rahoton Daily Trust, majiyoyi da yawa sun tabbatar da cewa kungiyoyin masu aikata laifuka guda biyu sun fara fafutukar neman matsayi a makon da ya gabata.

Wannan na zuwa ne makwanni uku bayan rufe hanyoyin sadarwa a jihar Zamfara, lamarin da ya tilastawa ‘yan ta’adda tserewa zuwa kauyukan Saulawa da Damari na karamar hukumar Birnin Gwari, inda suka kafa tutocinsu.

Wani mazaunin Birnin Gwari, Samaila Yakubu, wanda ya zanta da jaridar daga Zariya, ya ce rikicin tsakanin kungiyoyin masu laifi biyu ya biyo bayan umurnin da ‘yan ta’adda suka bayar.

Malam Yakubu ya ce ‘yan bindigar sun bijire wa doka, lamarin da ya kai ga tashin hankalin da ya yi sanadiyyar mutuwar’ yan bindiga hudu da wani dan kungiyar Ansaru a ranar Talata da ta gabata.

Ya ce an kai harin ta-tar-tat tsakanin kungiyoyin biyu wanda ya kai ga kashe ‘yan fashi 30 a makon da ya gabata.

Related posts

Leave a Comment