Rahotanni daga Jihar Sokoto na bayyana cewar wasu yan bindiga da ake tsammanin yan ?ungiyar sakai ne da aka haramta, sun hallaka mutum 11 a a kauyen Jihar Sokoto.
Rahotanni sun bayyana cewa akwai limamin masallaci daga cikin mutanen da maharan suka kashe a ?auyen Mamande, ?aramar hukumae Gwadabawa.
An ruwaito cewa baki ?aya mutanen sun mutu ne nan take, yayin da wasu mutum hu?u da suka jikkata aka kaisu asibiti domin duba lafiya.
Limamin da lamarin ya shafa, Malam Aliyu, an tabbatar da cewa shine yake jagorantar musulmai sallah a masallacin Salame.
Rahoto ya nuna cewa baki ?aya mutanen da aka kashe sun fito ne daga rugar fulani kala daban-daban, inda suka zo kasuwa siyan kayan abinci. Yan sakai sun farmaki kasuwar ba zato babu tsammani, kuma suka kashe mutanen, wa?anda suke zargi da tallafawa yan bindiga.
?aya daga cikin yan uwan limamin, Abdullahi Riskuwa, yace an kashe ?an uwansa ba tare da wata hujja ba domin bashi da wani kashin kaji a jikinsa. Riskuwa yace: “Yana da ilimin addinin musulunci kuma ya kasance yana limancin sallah a ?aya daga cikin masallatan mu na garin Salame.”
“Laifinsa ?aya ne, saboda ya kasance ?an kabilar fulani ne. Amma ba abinda yakai Aliyu kasuwa sai don ya sayi kayayyaki.”
Da aka tuntubi kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Sokoto, ASP Sanusi Abubakar, yace ba shi da masaniya kan lamarin. Gwamnan Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya haramta ayyukan yan sakai a fa?in jihar, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
