Rahotanni daga birnin Maiduguri fadar gwamnatin jihar Borno na bayyana cewar Wani mai daukar hoton bidiyo da ke aiki tare da kungiyar ta’addanci, Boko Haram, ya mika kansa ga jami’an gwamnati a jihar Borno da ke a Arewa maso gabashin Najeriya.
Mai daukar hoton bidiyon wanda har yanzu ba a bayyana sunansa ba, a halin yanzu yana tsare a wani gidan gwamnati tare da daruruwan sauran ‘yan ta’adda da suka mika wuya, HumAngle ta ruwaito.
Babban jami’in gwamnatin jihar Borno ya ce: “Yanzu muna da daya daga cikin manyan masu daukar hoton bidiyo da suka saba daukar bidiyon Boko Haram a hannunmu.”
“Ya mika kansa ga sojojinmu kuma ya fito da dukkan kayansa da suka hada da kwamfutocin tafi-da-gidanka da kyamarori masu inganci. Yana nan tare da mu kuma yana ba mu goyon baya sosai tare da bayanai kan yadda za a sa wasu su fito su kuma mika wuya.”
Mambobin kungiyar Boko Haram suna mika kansu a kullum. Jami’in ya kara da cewa: “Kamar yadda yake a yanzu, muna da mayaka sama da 790 wadanda a halin yanzu suna hannunmu bayan sun mika kansu da son ransu.”
A makon da ya gabata ne rundunar sojin Najeriya ta ce sama da mayakan Boko Haram 8000 da iyalansu sun mika wuya ga sojoji a Borno da wasu jihohin arewa maso gabas.
Sai dai majiyar ta yi karin haske da cewa “ba duk wadanda suka mika wuya ba ne ainihin mayakan Boko Haram.” A cewar majiyar: “Lokacin da ‘yan Boko Haram suka mika wuya sai suka fito tare da wasu mutane da yawa kamar matansu da yaransu, kamar manoma da aka tilasta su ci gaba da zama a yankunansu don yin aikin noma da sauransu.”
Majiyar ta ce ana kuma ci gaba da tantance na gaskiya da na karya a cikin tubabbun ‘yan ta’addan. Majiyar ta kara da cewa hatta mayakan na gaskiya sun taimaka wa jami’an gwamnati a wurin da ake tsare da su don gano ‘yan Boko Haram din da ba sa yaki ta hanyar tabbatar da ikirarin su na rashin aikata laifi.
