Zamfara: Mahaifin Shugaban Majalisa Ya Mutu A Hannun ‘Yan Bindiga

Rahotannin dake shigo mana daga Birnin Gusau babban birnin Jihar Zamfara na bayyana cewar Alhaji Abubakar, mahaifin kakakin majalisar dokokin jihar Zamfara, Hon. Nasiru Magarya ya mutu yayin da yake a tsare hannu masu garkuwa da mutane.

Mahaifin Kakakin wanda shine Hakimin kauyen Magarya, yan bindiga sun yi garkuwa da shi makwanni takwas da suka gabata, tare da matarsa, da kuma jariri dan makonni uku da haihuwa.

Yayin da aka ceto wadanda aka sace a jiya Asabar, mahaifin kakakin Majalissar baya cikin su.

Kazalika da yake jawabi ga manema labarai, babban yayan mamacin, Malam Dahiru Magarya, wanda yana cikin wadanda aka sace ya ce, mahaifin kakakin Majalissar ya rasu ne a hannun Yan bindigan, sakamakon bugun zuciya.

Sai dai har kawo hada wannan rahoto Gwamnatin jihar Zamfara da rundunar ‘yan sanda har yanzu ba su yi magana kan batun ba.

Kuma jaridar Puch ta ruwaito cewa, duk Kokarin da tayi na zantawa da kakakin majalisar abun ya ci tura, saboda an kasa samun lambobin wayarsa.

Related posts

Leave a Comment