Da Yiwuwar Mu Kakaba Dokar Ta Baci A Jihar Anambra – Ministan Shari’a

Rahotanni daga fadar Shugaban kasa dake babban birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnatin tarayyar ta ce za ta iya saka dokar ta-?aci a Jihar Anambra da ke kudancin ?asar domin tsaurara tsaro yayin gudanar da za?en gwamna a watan Nuwamba.

Ministan Shari’a Abubakar Malami ne ya bayyana hakan jim ka?an bayan kammala taron Majalisar Zartarwa ranar Laraba wanda Shugaba Buhari ya jagoranta.

Malami ya ce gwamnati za ta yi dukkan mai yiwuwa domin ta tabbatar da tsaron lafiyar mutane da dukiyoyinsu “idan gwamnatin jihar ta gaza yin hakan”.

“Idan aka samu tabbacin cewa gwamnatin jiha (Anambra) ba za ta iya kare rayukan mutane ba ta hanyar tabbatar da doka da oda gwamnatin tarayya za ta ?auki mataki kuma za mu iya saka dokar ta-?aci,” a cewarsa.

Matakin na zuwa ne yayin da ake ci gaba da samun rahotannin kashe-kashe a Anambra da kuma yankin kudu maso gabashin Najeriya.

An kashe mutum fiye da 10 a ‘yan makonnin da suka wuce a Anambra. Hukumar za?e ta ?asa INEC ta saka 6 ga watan Nuwamba domin gudanar da za?en gwamna a jihar.

Related posts

Leave a Comment