An bayyana matakan da gwamnatin Jihar Kaduna ?arkashin jagorancin Gwamna Nasiru El Rufa’i ta dauka na haramta hawa Babura da cin kasuwanni da sunan magance matsalar tsaro, a matsayin wani aiki da aka bar Jaki aka koma dukan taiki.
Bayanin hakan ya fito ne daga bakin wani jigo a siyasar Jihar Kaduna Alhaji Umar Ibrahim Mai Ra?umi, a yayin wata tattaunawa da yayi da manema labarai a Kaduna dangane da halin kunci da jama’ar Kaduna ke ciki tun bayan haramta hawa Babura a Jihar.
Mai Ra?umi wanda ya bada shawarar ?aukar matakan sulhu da ‘yan Bindiga a matsayin abin da ya dace fiye da matakin daukar makamai, inda ya bada misali da halin da tsaron ke cigaba da kasancewa tun bayan ?aukar matakan da aka yi.
Dangane da batun siyasar Najeriya bisa ga matsayar da babban jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta dauka na yin watsi da tsarin karba-karba, ?an siyasar ya bayyana cewar tun asali dama tsarin karba-karba bai cikin sharadi na siyasa, jam’iyyar PDP ce ta kirkiro shi domin wata manufa ta ta.
Ya bayyana cewar jama’a ne ke zabe ba jam’iyya ba, kuma yawan jama’ar Arewa tabbaci ne a gareta na tsayar da wanda take so ya shugabanci Kasa, bisa ga haka ba dole bane sai a wata kebabbiyar Jam’iyya za su yi takara, kamar PDP ko APC, akwai jam’iyyu masu yawa wanda dama ce a gare su.
