Rundunar sojin Najeriya ta sanar da kashe wani kwamandan kungiyar ISWAP Modu Kime wanda aka fi sani da Abou Maryam da wasu daga cikin mayakan kungiyar. Kafar yada labaran PRNigeria ta rawaito cewa, babban kwamandan ya gamu da ajalinsa a hare-hare ta sama da sojojin Najeriya suka kaddamar a Bisko da Tumbum Tawaye da ke karamar hukumar Abadam a yankin tafkin Chadi da ke jihar Borno. An yi nasara a harin ne bayan bayanan sirri sun sanar da sojojin maboyar masu tayar da kayar bayan. Wani jami’in tsaro ya shaida…
Read MoreCategory: Tsaro
Tsaro
Da Dumi-Dumi: An Damke Bakin Haure Cikin ‘Yan Bindiga
Hedikwatar Tsaro ta Sojojin Najeriya ta ce Sojojin Operation Whirl Stroke a Jihohin Benuwai, Nasarawa da Taraba sun kama ba?in-haure 16 da su ka tsallako daga Jamhuriyar Nijar su na kai hare-hare. Sanarwar ta ce an kama su a wurare daban-daban cikin jihohin tsakiyar Najeriya. Daraktan Ya?a Labarai na Hukumar Tsaron Najeriya Burgediya Janar Bernard Onyeuko ne ya yi wannan ?arin haske a ranar Alhamis a Abuja, lokacin da ya ke ?arin haske dangane da nasarorin da dakarun Najeriya ke ci gaba da samu a yankunan ?asar nan daban-daban.
Read MoreShure-Shure Boko Haram Suke Yi – Buhari
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar wa ?an Najeriya cewa daga yanzu saura kiris a gama da Boko Haram kwata-kwata a jihar Barno da yankin Arewa Maso Gabashin Najeriya. Idan ba a manta ba Jim ?adan kafin saukar jirgin saman shugaba Muhammadu Buhari, mahara da ake zaton ?an Boko Haram ?angaren ISWAP ne suka yi wa garin Maiduguri ruwan bamabamai. Duka unguwannin da bamabaman suka dira akan su na kusa da filin jirgin saman Maiduguri. Unguwannin da abin ya shafa sun ha?a da unguwar Ayafe, Ajilari Cross, Moromti rukunin gidajena…
Read MoreDa Dumi-Dumi: ‘Yan Sanda Sun Ceto ‘Yan Kasuwar Da Aka Sace A Kaduna
Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Rundunar ‘yan sandan jihar ta ce ta ceto ‘yan kasuwa 48 da aka sace a kan hanyarsu ta zuwa Kano a hanyar Birnin Gwari Jihar Kaduna ranar Laraba. Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ‘yan sandan jihar Kaduna, ASP Muhammad Jalige ya fitar a ranar yau Alhamis. Sanarwar ta bayyana cewa, a lokacin da ayarin motocin ‘yan kasuwar ke tunkarar kauyen Udawa, ‘yan bindiga dauke da bindigogi sun tari ‘yan kasuwar, lamarin da ya kai ga…
Read MoreDa Dumi-Dumi: ‘Yan Bindiga Sun Yi Gaba Da Masallata A Taraba
Rahotanni daga garin Tella da ke karamar hukumar Gassol a jihar Taraba a Najeriya na cewa wasu ‘yan bindiga sun sace mutane a masallacin garin. Jaridar Daily Trust ta ambato wani ganau na cewa ‘yan bindigar su 12 ne sukai wa masallacin kofar rago, a lokacin da mutanen suke yin sallar Isha a ranar Laraba. ‘Yan bindigar sun katse musu sallah tare da tasa keyarsu, amma daga bisani sun sako mutum guda. Cikin wadanda aka sace din akwai Alhaji Hussaini shugaban masu saida hatsi a yankin. Mai magana da yawun…
Read MoreDa Dumi-Dumi: ‘Yan Bindiga Sun Yi Gaba Da ‘Yan Kasuwa 70 A Kaduna
Rahoton dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar ?an ta’adda masu fashin daji sun yi garkuwa da ?an kasuwa sama da guda 70 a kan hanyar su ta zuwa Kano a titin Birnin-Gwari zuwa Kaduna a ranar Laraba. Jaridar Vanguard ta rawiato cewa an shaidawa manema labarai a Kaduna cewa ?an ta’addan sun tare jerin-gwanon motocin ?an kasuwan ne in da daga bisani su ka yi awon-gaba da su cikin jeji. Jaridar ta ce Rundunar ?an Sanda ta jihar ba ta ce komai a kan harin a daidai…
Read MoreZamfara: ‘Yan Bindiga Sun Arce Da Mutum 13 Dokar Daji
Rahotanni daga Gusau babban birnin Jihar Zamfara na bayyana cewar a kauyen Shemori na cikin karamar hukumar Gusau ‘yan bindiga sun sace mutum 13 ciki har da mata jiya da daddare. Mazauna yankin sun shaida wa BBC cewa ‘yan bindigar sun auka wa kauyen ne sakamakon gaza biyan harajin da suka dora musu. Shaidun da BBC ta zanta da su ta waya daga kauyen na Shemori sun ce a daren jiya ne maharan suka shiga garin a kan Babura. Wani mazaunin kauyen ya ce ‘yan bindigar sun auka musu ne…
Read MoreZan Tona Asirin Masu Daukar Nauyin ‘Yan Bindigar Jihata A Badi – Gwamnan APC
Labarin da muke samu daga Owerri babban birnin Jihar Imo na bayyana cewar Gwamna Hope Uzodimma ya sha alwashin bayyana sunayen wadanda ke da hannu wajen kai hare-hare a jihar Imo da suka yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama. PM News ta ruwaito cewa gwamnan ya bayyana haka ne a wani taron masu ruwa da tsaki da ya gudanar fadar gwamnatin jihar makon da ya gabata. Ya yi bayanin cewa wasu mutane 18 ne da jami’an tsaro suka kama kwanan nan kan kashe kansiloli biyu a jihar, suka bayyana sunayen…
Read MoreNeja: ‘Yan Bindiga Sun Tilasta Rufe Makarantu
Rahotanni daga Jihar Neja na bayyana cewar Gwamnatin jihar ta bayar da umarnin rufe duka makarantun firamare da sakandire da na gaba da sakandire a ?aramar Hukumar Wushishi da ke jihar. An ruwaito Shugaban ?aramar Hukumar Wushishi, Danjuma Suleiman Nalango inda shi ne ya bayar da umarnin sakamakon zargin da ake yi na yun?urin sace ?alibai a Zungeru da makwafta. Shugaban ?aramar hukumar ya shaida cewa an samu bayanan sirri daga hukumomin tsaro a kan lamarin na yun?urin ?an bindiga shiga kwalejin kimiyya da fasaha da makarantar ?an mata ta…
Read MoreZamfara: Shugaban ‘Yan Bindiga Turji Ya Gindaya Sharuddan Tuba
Rahotannin dake shigo mana daga Gusau babban birnin Jihar Zamfara na bayyana cewar Sanannen ?an bindigan nan da ya addabi yankunay Jihohin Zamfara, Sokoto da Katsina Bello Turji, ya nemi a yi zaman sulhu domin kawo karshen kashe-kashe a yankunan. A wasikar da ya aike wa shugaban kasa Buhari, gwamna Matawalle, da Sarkin Shinkafi, Turji, ya sha alwashin aje makamansa bisa wasu sharu??a da ya gindaya. A kwafin wasikar mai shafi uku, ?auke da kwanan watan 14 ga watan Disamba. ?an ta’addan ya nemi a yi wasu yarjejeniyoyi kafin ya…
Read MoreDuk Dan Bindigar Da Ya Yi Gigin Shiga Jihata Zai Bakunci Lahira – Gwamnan Kogi
Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya sha alwashin ?aukar tsattsauran mataki kan Yan ta’addan Daji Matukar Suka Shigo Masa jiha.. Gwamna Bello ya yi wannan furucin ne yayin da ya kar?i bakuncin shugaban ?aramar hukumar Yagba West, Pius Kolawole, domin tattaunawa kan fashi da makami a yankinsa da kuma matakan da aka ?auka. Gwamnan Ya ?ara jaddada kudirin gwamnatinsa na ha?a kai da dukkan hukumomin tsaro wajen tsaftace jihar daga mutane masu tunanin aikata ta’addanci ba tare da tausayi ba.
Read More‘Yan Bindiga Na Addabar Jihar Kaduna – Kwamishinan Tsaro
Kwamishinan tsaron jihar Kaduna Samuel Aruwan ya bayyana cewa ‘yan bindiga sun kashe mutum 9 sannan sun ji wa biyu sun ji rauni a kananan hukumomin Chikun, Zaria, Igabi da Zangon Kataf. Aruwan ya kara da cewa gwamnati ta samu labarin haka ne daga bayanan da jami’an tsaro dake aiki a jihar suke sanar mata. Aruwan ya ce ‘yan bindiga sun kashe mutum uku a kauyen Buruku-Udawa a dalilin rufe hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari da suka yi a karamar hukumar Chikun. “Maharan sun kashe Umma Ibro-Kontagora, Abdullahi Noma-Kontagora da…
Read MoreMatsalar Tsaro: Fito Na Fito Da ‘Yan Bindiga Ne Mafita – Masari
Gwamna Aminu Masari na Jihar Katsina, ya ce ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane da kashe mutane, sun fi dabbobi dabbanci. Masari ya bayyana haka a Sokoto, lokacin da ya jagoranci tawagar Gwamnonin Arewa maso Yamma, inda su ka je ta’aziyyar mutane 23 matafiya da ‘yan bindiga su ka banka wa wuta a cikin mota, su ka ?one ?urmus. Masari ya ce jami’an tsaro su ka?ai ba za su iya kawar da ‘yan bindiga ba. A kan haka ne ya ce lokaci ya yi da jama’a za su tashi su…
Read MoreSarautar Yusuf Buhari: Manyan Kasa Sun Taru Birnin Daura
An na?a Yusuf Buhari ?an gidan Shugaban ?asa Muhammadu Buhari sarautar Talban Daura a masarautar Daura a ranar Asabar. Mataimakin Sugaban ?asa Farfesa Yemi Osinbajo da Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan da sauran manyan ba?i, kamar su gwamnan Katsina Aminu Bello Masari da Sarkin Bichi Nasiru Ado Bayero duk sun isa garin Daura domin halartar taron na?in sarautar da za a yi wa ?an Shugaba Muhammadu Buhari. Masarautar ta Daura, wadda ita ce mahaifar Shugaba Buhari, ta na?a Yusuf Buhari a matsayin Talban Daura kuma Hakimin Kwasarawa. Sarkin Daura Alhaji…
Read MoreKimanin Jami’an Tsaro 1000 Aka Kashe Cikin Shekara 1000 Guda – Rahoto
Wani rahoto da wata cibiyar tattara bayanan sirri ta SB Morgen Intelligence ta wallafa ta ce an kashe jami’an tsaro a Najeriya da suka kai 966 a shekara guda. Cibiyar ta saki rahoton ne a ranar Alhamis, bayan tattara bayanan sirrin da ta yi na hare-hare da aka kai wa jami’an tsaro daga watan Oktoban 2020 zuwa Satumbar 2021. Rahoton ya bayyana ma’anar ya?i a matsayin duk wani rikici da aka kashe mutum a?alla 1,000. “Saboda wannan za mu iya cewa Najeriya na cikin ya?i,” a cewar rahoton. Zuwa yanzu…
Read MoreKaduna: ‘Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Hari Birnin Zazzau
Labarin dake shigo mana daga Birnin Zazzau na Jihar Kaduna na bayyana cewar wasu ‘yan bindiga sun sake kai hari, inda suka kashe wani Alhaji Habibu na yankin Sayen Lemu a Dutsen Abba na karamar hukumar Zariya a jihar Kaduna tare da yin garkuwa da ‘ya’yansa uku. Sayen lemu wani kauye ne da ke kusa da Nuhu Bamalli Polytechnic, Zariya, kuma yana da tazarar kilomita 5 daga inda ‘yan bindiga suka tare hanyar Kaduna zuwa Zariya a ranar Litinin. Rahotanni sun ce ‘yan bindigan sun isa gidansa da misalin karfe…
Read MoreTsaro: China Ta Lashi Takobin Kawar Da ‘Yan Ta’addan Najeriya
?asar China ta ce za ta tura tawaga ta musamman ta ?wararru kan binciken laifuka domin tattaunawa da hukumomin tsaron Najeriya. Jakadan ?asar China a Najeriya Cui Jianchun ne ya sanar da hakan a ranar Laraba inda ya ce China za ta yi haka ne saboda ta damu kan matsalolin tsaron da Najeriyar ke fama da su. Mista Cui ya bayyana cewa wannan yun?urin da China ke yi na daga cikin goyon bayan da take ba ?asar wajen magance matsalolin tsaro inda ya ce nan ba da jimawa ba ?wararrun…
Read MoreTsaro: Za A Kone Dubban Babura A Abuja
Labarin dake shigo mana yanzu haka daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Rundunar ?an sanda reshen Abuja da kuma hukumar kula da lafiyar ababen hawa VIO da wasu hukumomi sun ha?a hannu domin ?ona babura 1,500. Sun bayyana cewa za a ?ona baburan ne domin jama’a na amfani da su wajen aikata laifuka kuma tuni an haramta amfani da su a cikin ?waryar Abuja. Hukumomin sun ce duk da haramcin amma ana samun masu kunnen ?ashi suna karya dokoki wanda hakan ya sa za su ?ona baburan domin koya…
Read MoreMummunan Rikicin Cikin Gida Ya Barke Tsakanin ‘Yan Bindiga
Rahotanni dake shigo mana yanzu haka na bayyana cewar wani mummunan rikicin cikin gida da ya ?arke tsakanin yan bindiga a karamar hukumar Batsari jihar Katsina da abokan adawarsu na jihar Zamfara na ?ara kamari. Majiyar Aminiya ta tabbatar da cewa ‘yan bindigan Batsari na kame duk wani ?an bindiga da suka gani ya shigo yankinsu daga jihar Zamfara. A cewar majiyar, ?auyukan Nahuta, Madogara, Zamfarawa da Tashar Modibbo da sauran wasu ?ananan kauyuka duk suna karkashin ?an bindiga, Abu Radda. Kuma jagoran yan bindigan ya umarci yaransa su cafke…
Read MoreHari Gidan Alkalin Babbar Kotu: An Gurfanar Da Wadanda Ake Zargi
An gurfanar da wasu mutane 15 gaban wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, bisa zargin kutsa kai gidan mai shari’a ta kotun kolin Mary Odili a cikin watan Oktoban da ya gabata. Ana zargin mutanen, wa?anda suka bayyana kansu a matsayin jami’an tsaro, sun kutsa kan su gidan ne, da nufin gudanar da bincike, bisa zargin ana aikata wasu abubuwa da suka sa?a doka a cikin gidan. A cikin watan Nuwamban da ya gabata ne, rundunar ?an sanda ta gabatar wa manema labarai, mutanen 15 da ake zargi da…
Read More