Rikicin Jam’iyya: Ya Zama Dole APC Ta Dauki Darasi Daga PDP – Buhari

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban ?asa Buhari ya yi garga?i ga ?a?an Jam’iyyar APC kan rikicin shugabanci da ya dabaibaiye jam’iyyar.

A bayanin da ya wallafa a shafin Facebook, Buhari ya yi kira ga ?an jam’iyyarsa da su guji ko?arin tayar da zaune tsaye a APC kafin babban taronta na ranar 26 ga watan Maris.

A cikin sa?on Buhari wanda yake hutu a birnin Landan bai ambaci ?angarorin biyu ba da kuma jayayyar da suke ta shugabancin ri?o na APC.

Sai dai shugaban ya ala?anta da kamanta rikicin jam’iyyar hamayya ta PDP, yana mai cewa ya kamata ya zama darasi ga APC.

“Dole mu kalli PDP mai ?arfi a baya da yanzu ta tarwatse, kuma mu koyi darasi da rashin ha?in kansu da rashin iya gudanar da mulki da kuma rashawa,” in ji Buhari.

Buhari ya kuma bayyana rikicin da abin da ya kira raba hankalin jam’iyyar gabanin babban taronta na za?en shugabanni. Ya ce ha?in kai ne zai zama tsanin ci gaba da samun nasarar jam’iyyar a dukkanin ?angarori na Najeriya.

Related posts

Leave a Comment