?asar China ta ce za ta tura tawaga ta musamman ta ?wararru kan binciken laifuka domin tattaunawa da hukumomin tsaron Najeriya.
Jakadan ?asar China a Najeriya Cui Jianchun ne ya sanar da hakan a ranar Laraba inda ya ce China za ta yi haka ne saboda ta damu kan matsalolin tsaron da Najeriyar ke fama da su.
Mista Cui ya bayyana cewa wannan yun?urin da China ke yi na daga cikin goyon bayan da take ba ?asar wajen magance matsalolin tsaro inda ya ce nan ba da jimawa ba ?wararrun za su isa Najeriyar.
