Rahotanni daga Jihar Neja na bayyana cewar Gwamnatin jihar ta bayar da umarnin rufe duka makarantun firamare da sakandire da na gaba da sakandire a ?aramar Hukumar Wushishi da ke jihar.
An ruwaito Shugaban ?aramar Hukumar Wushishi, Danjuma Suleiman Nalango inda shi ne ya bayar da umarnin sakamakon zargin da ake yi na yun?urin sace ?alibai a Zungeru da makwafta.
Shugaban ?aramar hukumar ya shaida cewa an samu bayanan sirri daga hukumomin tsaro a kan lamarin na yun?urin ?an bindiga shiga kwalejin kimiyya da fasaha da makarantar ?an mata ta sakandire duka da ke a wajen garin Zungeru.
Ya bayyana cewa an ?auki wannan matakin ne domin guje wa irin abin da ya faru a Tegina inda a kwanakin baya aka sace ?aliban islamiyya.
