Mummunan Rikicin Cikin Gida Ya Barke Tsakanin ‘Yan Bindiga

Rahotanni dake shigo mana yanzu haka na bayyana cewar wani mummunan rikicin cikin gida da ya ?arke tsakanin yan bindiga a karamar hukumar Batsari jihar Katsina da abokan adawarsu na jihar Zamfara na ?ara kamari.

Majiyar Aminiya ta tabbatar da cewa ‘yan bindigan Batsari na kame duk wani ?an bindiga da suka gani ya shigo yankinsu daga jihar Zamfara. A cewar majiyar, ?auyukan Nahuta, Madogara, Zamfarawa da Tashar Modibbo da sauran wasu ?ananan kauyuka duk suna karkashin ?an bindiga, Abu Radda.

Kuma jagoran yan bindigan ya umarci yaransa su cafke duk wani bakon ?an bindiga ko barawo da suka gani ya shigo yankunan ba tare da izini ba.

Haka nan kuma Abdu Mai Komi, wani ?an bindiga mai iko da yankunan Gobirawa, Garin Runji, Garin Yara, Kondatso da Yasure, shi ma ya ha?a kai da Abu Radda wajen kame duk wasu bakin yan bindiga da suka shigo.

Wani rahoto ya nuna cewa yaran wani ?an Bindiga daga Zamfara, Dangote, su ke yawan kai hare-hare yankin Batagarawa a Katsina. Sai dai a hanyarsu ta komawa gida, yaran Abu Radda da na Abdu Mai Komai suka yi musu kwanton bauna suka kashe na kashewa suka kwace dabbobin da suka sato.

Wasu daga cikin mazauna kauyukan dake yankim Ruma Tsohuwa sun shaida yadda tawagar yan bindigan biyu suka fafata da junansu.

“Bayan sun kwace shanu da makaman yan bindigan, sun raba a tsakanin su da wasu da suka taimaka musu.” A halin yanzun, rikicin ya yi ?amari matuka ta yadda ba wanda ke yawo da bindiga don gudun kada a farmake shi.

Kakakin rundunar yan sanda resehn jihar Katsina, SP Gambo Isa, yace hukumar yan sanda ba ta da masaniya amma zata bincika domin gano gaskiya.

Related posts

Leave a Comment