Tsaro: Za A Kone Dubban Babura A Abuja


Labarin dake shigo mana yanzu haka daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Rundunar ?an sanda reshen Abuja da kuma hukumar kula da lafiyar ababen hawa VIO da wasu hukumomi sun ha?a hannu domin ?ona babura 1,500.

Sun bayyana cewa za a ?ona baburan ne domin jama’a na amfani da su wajen aikata laifuka kuma tuni an haramta amfani da su a cikin ?waryar Abuja.

Hukumomin sun ce duk da haramcin amma ana samun masu kunnen ?ashi suna karya dokoki wanda hakan ya sa za su ?ona baburan domin koya wa wa?anda suka karya doka darasi.

Related posts

Leave a Comment