Da Dumi-Dumi: ‘Yan Bindiga Sun Yi Gaba Da Masallata A Taraba

Rahotanni daga garin Tella da ke karamar hukumar Gassol a jihar Taraba a Najeriya na cewa wasu ‘yan bindiga sun sace mutane a masallacin garin.

Jaridar Daily Trust ta ambato wani ganau na cewa ‘yan bindigar su 12 ne sukai wa masallacin kofar rago, a lokacin da mutanen suke yin sallar Isha a ranar Laraba.

‘Yan bindigar sun katse musu sallah tare da tasa keyarsu, amma daga bisani sun sako mutum guda. Cikin wadanda aka sace din akwai Alhaji Hussaini shugaban masu saida hatsi a yankin.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Taraba DSP Usman Abdullahi ya tabbatar da kai wannan harin.

Cikin makwanni uku da suka gabata, ‘yan bindiga sun sace sama da mutane 25, yawancinsu ‘yan kasuwa daga sassa daban-daban na jihar.

Tun bayan zafafa hare-hare da sojoji suka yi a jihar Zamfara, ya janyowa mazun karmar hukumar Gassol rashin zaman lafiya ind ‘yn bindiga ke kai hare-hare da satar mutane domin neman kudin fansa

Related posts

Leave a Comment