An na?a Yusuf Buhari ?an gidan Shugaban ?asa Muhammadu Buhari sarautar Talban Daura a masarautar Daura a ranar Asabar.
Mataimakin Sugaban ?asa Farfesa Yemi Osinbajo da Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan da sauran manyan ba?i, kamar su gwamnan Katsina Aminu Bello Masari da Sarkin Bichi Nasiru Ado Bayero duk sun isa garin Daura domin halartar taron na?in sarautar da za a yi wa ?an Shugaba Muhammadu Buhari.
Masarautar ta Daura, wadda ita ce mahaifar Shugaba Buhari, ta na?a Yusuf Buhari a matsayin Talban Daura kuma Hakimin Kwasarawa.
Sarkin Daura Alhaji Umar Farouk wanda shi ne Sarkin na Daura shi ne ya yi wannan na?in mai tarihi a ranar Asabar.
Gwamna Aminu Bello Masari na Katsina ne ya tar?i Ahmad Lawan a filin jirgi na Katsina.
Sai dai ana wannan bikin ne a yayin da shugaba kasa Buhari ke Turkiyya inda yake halartar taron cinikayya tsakanin Turkiyya da Afrika.
A wannan shekarar ne Talban na Daura ya auri Zahra Nasir Ado Bayero wadda ?a ce ga Sarkin Bichi.
