Kaduna: ‘Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Hari Birnin Zazzau

Labarin dake shigo mana daga Birnin Zazzau na Jihar Kaduna na bayyana cewar wasu ‘yan bindiga sun sake kai hari, inda suka kashe wani Alhaji Habibu na yankin Sayen Lemu a Dutsen Abba na karamar hukumar Zariya a jihar Kaduna tare da yin garkuwa da ‘ya’yansa uku.

Sayen lemu wani kauye ne da ke kusa da Nuhu Bamalli Polytechnic, Zariya, kuma yana da tazarar kilomita 5 daga inda ‘yan bindiga suka tare hanyar Kaduna zuwa Zariya a ranar Litinin.

Rahotanni sun ce ‘yan bindigan sun isa gidansa da misalin karfe 11 na daren Laraba inda suka harbe shi har lahira sannan suka yi awon gaba da ‘ya’yansa uku.

Majiyar ta shaida cewa: “Ba mu tunanin an turo a kashe shi ne. Mun yi imanin cewa suna cikin ‘yan bindigan da ke ta’addanci a yankin a baya-bayan nan.” “Kun san wannan yanki yana da yawan samun hare-hare daga ‘yan bindiga a cikin shekara guda, amma duk da haka ba a dauki matakin ceto rayukanmu daga hare-haren da suke kai wa ba.”

Idan baku manta ba, a ranar Laraba ne wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da mutane biyar a yankin Dallatu da Kasuwar Da’a da ke Dutsen Abba a Zariya. Lamarin ya faru ne sa’o’i 24 bayan ‘yan bindiga sun tare hanyar Kaduna zuwa Zariya tare da kashe mutane uku da yin awon gaba da mutane da dama.

Related posts

Leave a Comment