Zamfara: Shugaban ‘Yan Bindiga Turji Ya Gindaya Sharuddan Tuba

Rahotannin dake shigo mana daga Gusau babban birnin Jihar Zamfara na bayyana cewar Sanannen ?an bindigan nan da ya addabi yankunay Jihohin Zamfara, Sokoto da Katsina Bello Turji, ya nemi a yi zaman sulhu domin kawo karshen kashe-kashe a yankunan.

A wasikar da ya aike wa shugaban kasa Buhari, gwamna Matawalle, da Sarkin Shinkafi, Turji, ya sha alwashin aje makamansa bisa wasu sharu??a da ya gindaya.

A kwafin wasikar mai shafi uku, ?auke da kwanan watan 14 ga watan Disamba. ?an ta’addan ya nemi a yi wasu yarjejeniyoyi kafin ya aje makamai.

Muhimman abubuwa hudu da kasurgumin dan bindiga, Bello Turji, ya nema a wasikar sulhun sune kamar haka:

1. Gwamnati ta soke kungiyar yan sa’kai A cewarsa matukar gwamnati ta rushe ?ungiyar yan sa’kai to da izinin Allah duk wasu kashe-kashe da yan bindiga ke yi ya zo ?arshe. Haka nan kuma yace dole sai an cire ?abilanci da ake nuna musu (wato fulani) a koma ?asa ?aya dun?ulalliyar kamar yadda take a baya.

2. ?azalika a wasikar sa, Turji, ya nemi masarautar Shinkafi ta shirya musu zama da sarakunan ?asar nan da kuma manyan malamai domin tattaunawar adalci. Ya yi al?awarin matukar aka shirya wannan zama, to zai karbi duk wata bindiga da ake aikata ta’addanci da ita ya mi?a wa hukumomin gwamnatin Najeriya. “Idan haka ta samu (Zaman Sulhu) to ni Muhammad Bello Turji Kachalla, na yi al?awarin zan karbi dukkan bindigun da ake aikata ta’addanci da su na mi?a wa gwamnatin Najeriya.”

3. Sanannen ?an bindigan ya ?ara tabbatarwa sarkin Shinkafi da gwamna Matawalle cewa su ba fa?a da gwamnati suke son yi ba, kuma ba wata ?ungiya suke yunkurin kafawa ba. Ya bayyana cewa cin zarafin da ake wa Fulani yan uwansu a fa?in ?asar nan da nuna musu bambanci shine ummul aba’isin wannan abubuwan na rashin zaman lafiya.

4. Abu na ?arshe kamar yadda ya rubuta a wasikarsa, Turji yace yayin zaman sulhu suna bukatar a ha?a manyan sarakuna da manyan malaman ?asar nan baki ?aya, kuma suna bukatar ganin Sheikh Ahmad Abubakar Gumi. Bugu da ?ari, yace sun san Sheikh Gumi, ya taba zuwa har inda suke ya musu waazi kuma wa’azinsa ya musu amfani, shiyasa suke son zaman lafiya.

Daga ?arshe Turji yace wannan ne dalilinsa na rubuta wannan wasi?a kuma dagaske yake ba da yaudara ba, kamar yadda baya son a yaudare su.

Related posts

Leave a Comment