Matsalar Tsaro: Fito Na Fito Da ‘Yan Bindiga Ne Mafita – Masari

Gwamna Aminu Masari na Jihar Katsina, ya ce ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane da kashe mutane, sun fi dabbobi dabbanci.

Masari ya bayyana haka a Sokoto, lokacin da ya jagoranci tawagar Gwamnonin Arewa maso Yamma, inda su ka je ta’aziyyar mutane 23 matafiya da ‘yan bindiga su ka banka wa wuta a cikin mota, su ka ?one ?urmus.

Masari ya ce jami’an tsaro su ka?ai ba za su iya kawar da ‘yan bindiga ba.

A kan haka ne ya ce lokaci ya yi da jama’a za su tashi su kare kan su. Ya ce ta haka ne kawai za a iya taimakon jami’an tsaro a mur?ushe ‘yan bindiga.

A na sa jawabin, Gwamna Aminu Tambuwal na Sokoto ya ce kafa wa ‘yan bindiga dokar-ta-?aci ne ka?ai zai iya sa sojoji su gama da su baki ?aya.

Gwamna Aminu Tambuwal na Jihar Sokoto, kafa dokar-ta-?aci a kan ‘yan bindiga ne ka?ai zai iya bai wa sojoji damar kutsawa cikin dazuka, su yi kan-mai-uwa-da-wabi, domin su kakka?e ‘yan bindiga.

Tambuwal ya yi wannan shawara ce ranar Laraba a Sokoto, lokacin da ya ke kar?ar tawagar Gwamnonin Jihohin Arewa maso Yamma.

Tawagar wadda ke ?ar?ashin Gwamna Aminu i na Katsina, sun je Sokoto ne domin yin ta’aziyyar matafiya 23 da ‘yan bindiga su ka banka wa wuta, su ka ?one ?urmus.

Tambuwal ya ro?i Shugaba Muhammadu Buhari ya kafa dokar-ta-?aci, domin ta haka ne “za a bai wa jami’an tsaro ?arfin umarnin bisa doka, yadda za su yi amfanin da dukkan ?arfin sojoji su mur?ushe ‘yan bindiga.”

Tambuwal ya ce yin wannan dokar ce za ta bai wa sojoji damar yin amfani da duk wani ?arfin soja, ba tare an ri?a ?orafin cewa sun take ha??in jama’a ba.

“‘Yan bindiga ba su da wani ?angaren addini da su ka yi ri?o ko ?abilanci ba. Kawai hatsabibin ma?arnata ne, masu ta’addanci.” Inji Tambuwal.

Haka kuma Tambuwal ya bada shawara cewa gwamnatin tarayya ta hanzarta horas da matasan yankunan da ‘yan bidindiga su ke, domin su ri?a yin aikin samar da tsaro.

Matasan ya kasance Zaratan Tsaron Musamman ne, kuma a horas da su sarrafa makamai, ta yadda za su ri?a tunkarar ‘yan bindiga.

“Bayan an samu nasara, sai a maida wa?annan matasa jami’an tsaron dazuka ta yadda wasu ‘yan bindiga ba za su sake bayyana ba.

“Mu a Sokoto mun haramta ‘yansakai, wa?anda aikin su ya na wuce gona-da-iri, su na kashe wa?anda ba su da wata ala?a da garkuwa da mutane.

“Irin wa?annan kashe-kashen ne ke harzu?a ‘yan bindiga zuwa ?aukar fansa a garuruwan da ‘yansakai su ke.” Inji Tambuwal, wanda ya ce hakan ne kuma ya ?ara ruruta wutar wannan fitina.

Ya ce ya kamata kowa ya sa hannu a taimaki wannan gwamnati domin shawo kan wannan masifa.

Daga nan kuma ya ro?i mutane su ri?a fallasa masu mugun hali a cikin su, ta hanyar gaggauta shaida wa jami’an tsaro.

Related posts

Leave a Comment