Hukumar kula da filayen jiragen sama ta Najeriya ta kammala shirye-shiryen rufe filin jirgin saman jihar Kebbi da ke Birnin-Kebbi, saboda gaza biyan bashin da ya kai naira miliyan 33. Rahotanni sun nuna cewa tuni Hukumar da ke kula da sararin samaniya ta Najeriya ta umurci kamfanonin jiragen sama da su kauracewa filin jirgin mallakar gwamnatin jihar Kebbi ba tare da ba ta lokaci ba. Wata majiya ta ce tuni FAAN ta kwashe ma’aikatan kwana-kwana da kuma masu ba da tsaro a filin jirgin. Ana zargin gwamnatin jihar Kebbi da…
Read MoreCategory: Tattalin Arziki
Tattalin Arziki
Kaduna: Tsoffin ‘Yan Sanda Sun Yi Zanga-Zangar Rashin Fansho
Rahotanni dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar wasu Jami’an ‘yan sanda masu murabus a jihar sun fito zanga-zangar lumana ga hukumar fansho dake Jihar sakamakon mawuyacin halin da suke ciki. Tsofaffin ‘yan sanda sun yi tattaki zuwa hedkwatar rundunar ‘yan sanda da ke Kaduna domin mika kokensu Sun dade suna korafin yadda hukumar fansho ke nuna musu mugunta tare da rashin tausayi wurin rike musu kudi. Daga karshe dai tsofaffin ‘Yan sandan da sun fita zanga-zangar lumana kan rike musu kudade da hukumar fansho ta jihar Kaduna…
Read More‘Yan Damfara Na Amfani Da Bitcoin Wajen Damfarar Jama’a – Shugaban EFCC
Shugaban Hukumar Yaki da Yiwa Tattalin Arzikin Kasa Zagon Kasa (EFCC) Abdulrasheed Bawa, ya ce kudaden intanet sun zama wani zabi ga mutanen da ke gudanar da hada-hadar kudi ba bisa ka’ida ba. Bawa ya fadi hakan ne yayin da yake gabatar da jawabi a ranar Litinin 6 ga watan Satumba, a taron kasa da kasa na Cambridge karo na 38 kan laifukan tattalin arziki, mai taken, ‘Laifin Tattalin Arziki: Wa Ya Biya kuma Wa Ya Kamata Ya Biya Farashi?’ Cibiyar Adana Bayanai ta Duniya kan Tsararrun Laifukan Tattalin Arziki…
Read MoreDa Wuya A Daina Fasa Kwabrin Fetur A Najeriya – NNPC
Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban kamfanin matatan man fetur na Nigeria, NNPC, ya ce kamfanin da wasu hukumomin tarayya za su cigaba da fama da kallubalen fasakwabrin kayayyakin man fetur saboda babancin farashin man fetur a Nigeria da kasashen da ke makwabtaka da ita. An ruwaito Shugaban NNPC, Mele Kyari ya sanar da hakan yayin wani jawabi da ya yi wurin taron tattaunawa da kwamitin Majalisar Dattijai na tsara yadda ake kashe kudade ta shirya. A cewar wata sanarwa da shugaban sashin hulda da jama’a na…
Read MoreAbuja: Kotu Ta Yi Fatali Da Bukatar Maina
Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta ki sauraron bukatar belin tsohon shugaban PRTT, Abdulrasheed Maina. Alkalin kotun Justice Ahmed Mohammed, ya ki sauraron sabuwar bukatar da lauyan Maina, David Iorhemba ya gabatar gare shi, na neman a bada belin tsohon shugaban hukumar kula da ku?a?en Fansho na ?asa. Yayin da Iorhemba ya bukaci kotu ta bayar da belin tsohon shugaban PRTT, lauyan EFCC, A. M. Ocholi ya ce ya shigar da karar da ta ci karo da wannan bukatar. Justice Mohammed…
Read MoreBuhari Ya Kaddamar Da Shirin Samar Wa Matasa Ayyukan Yi
Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban ?asa, Muhammadu Buhari, ya roki matasan Najeriya su shiga sabon shirin “Jubilee Fellows Programme,’ wanda zai samar wa masu kwalin digiri 20,000 aikin yi. Shugaban ya fa?i haka ne yayin kaddamar da shirin a fadarsa dake babban birnin tarayya Abuja, ranar Talata. An ruwaito cewa shirin zai ?auki matasa wa?anda ba su haura shekara 30 a duniya ba, kuma zai kwashe watanni 12. Mai taimakawa shugaban ?asa, Buhari Sallau, ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa shirin zai samar wa matasan…
Read MoreTattalin Arzikin Najeriya Ya Cilla Sama – Rahoto
Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar tattalin arzikin Najeriya ya karu da kashi 5.01 a tsakanin watan Afirilu zuwa watan Yuni na 2021 daga kashi 0.51 da aka samu a watanni uku na farkon shekarar nan ta 2021. Rahoton daukacin kayan aiki da kasar nan ta samar na watanni uku wanda NBS ta fitar a ranar Alhamis ya nuna cewa wannan cigaban na kashi 5.01% shine mafi girma da aka taba samu tun daga karshen shekarar 2014, Shekaru Bakwai. Wannan habakar tattalin arzikin ya fi na wancan shekarar…
Read MoreGwamnatin Tarayya Ta Kaddamar Da Shirin N-Power Karo Na Uku
Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnatin tarayya a ranar Litinin 23 ga watan Agustan 2021 ta fara kaddamar da shirin N-Power rukunin C shashi na farko. Ma’aikatar agaji da ayyukan jin kai ta kasa ta fara aikin yin rajista na rukuni na uku na masu cin gajiyar shirin a ranar 26 ga Yuni, 2020. Ministar agaji da ayyukan jin kai, Sadiya Farouq ta ce sama da mutum miliyan shida suka nuna sha’awarsu ga cin gajiyar shirin. Ta ce rukunin C zai dauki mutane 510,000 don cin gajiyar…
Read MoreMa’aikatar Sadarwa Ta Tara Sama Da Tiriliyan Guda A Shekara Biyu – Pantami
Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Ma’aikatar sadarwa da tattalin arzikin zamani tace ?angaren fasahar zamani (ICT) zai kara yawan ku?a?en shiga da yake samarwa gwamnatin tarayya domin habbaka tattalin arzikin ?asa. Ministan sadarwa, Sheikh Isa Pantami, shine ya fa?i haka yayin zantawa da kamfanin dillancin labarai na ?asa (NAN) a Abuja ranar Lahadi. Ministan ya jaddada amfani ICT wajen farfado da tattalin arzikin Najeriya, yace ?angaren na ICT shine yafi kowane ?angare cigaba cikin kankanin lokaci. Minista Pantami ya kara da cewa Najeriya ta cigaba da tsammanin…
Read MoreEFCC Ta Fara Bibiyar Sawun Kwankwaso
Rahotanni daga Jihar Kano na bayyana cewar Hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta rufe wasu dukiyoyi mallakar Sanata Rabiu Kwankwaso a jihar Kano, cikin gaggawa ba tare da bata lokaci ba. An ruwaito cewa daya daga cikin wadanda ke kusa lokacin da jami’an EFCC suka zo don rufe ginin ya yi tsokaci: Ya bayyana cewa jami’an sun shaida musu cewa rufewar ya biyo bayan wata takardar korafi da hukumar ta samu daga iyalan Ismaila Gwarzo, tsohon mai ba da shawara kan harkokin tsaro. “Batun rufe…
Read MoreBabu Wani Cigaban Da Najeriya Ta Samu A Tsawon Shekaru 40 – Sunusi
Tsohon Sarkin Kano Alhaji Muhammad Sanusi ll ya ce Najeriya ba ta samu wani cigaba ba cikin shekaru 40, na azo a gani tun daga kan mulkin shugaban kasa Shagari har zuwa yanzu. Sanusi ya fadi haka ne a wani taron tattaunawa na murnar cikarsa shekaru 60 a duniya da aka gabatar ranar Asabar 14 ga watan Agusta 2021 a garin Kaduna. Tsohon Gwamnan na Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ce akwai bukatar ci gaba a fannin tattalin arzikin kasa, amma abin ba?in ciki da takaici babu wani cigaba ta…
Read MoreKotu Ta Ba EFCC Damar Rike Miliyoyin Da Aka Wawure A Asusun Gwamnatin Tarayya
Rahotanni daga birnin Ikko na Jihar Legas na bayyana cewar wata babbar kotun tarayya mai zama a garin Legas ta zartar da cewa a karbe wasu kudi da aka karkatar daga ofishin hadimin shugaban kasa a mayar dasu ga Hukumar EFCC. Ana zargin an yi awon gaba da N241m Alkali mai shari’a Nicholas Oweibo ya bada umarni a rike Naira miliyan 241 da aka yi gaba da su daga ofishin mai ba shugaban kasa shawara a kan harkokin siyasa. Alkalin ya kuma yanke hukunci cewa a karbe wasu shaguna da…
Read MoreKyari: Har Yanzu Ba Mu Karbi Wata Takarda Daga Amurka Ba – Ministan Shari’a
Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Ofishin Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya, kuma ministan Shari’a Abubakar Malami, ta ce har yanzu ba ta karbi wata takarda a hukumance daga cibiyar binciken Amurka ta FBI ba da ke neman damar kame mataimakin kwamishinan ‘yan sanda, Abba Kyari. Wannan ya fito ne daga bakin mataimaki na musamman ga ministan, Umar Gwandu yayin wata tattaunawa ta wayar tarho da wakilin jaridar Punch. FBI ta zargi Abba Kyari da karbar cin hanci daga hannun Hushpuppi, wani dan damfara dake fuskantar zaman kotu a…
Read MoreDa Dumi-Dumi: EFCC Ta Yi Nasarar Kama Saraki
Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar a yau Asabar ne hukumar EFCC suka cafke tsohon shugaban majalisar Dattawa, Bukola Saraki domin tuhumar sa akan harkallar wasu ku?a?e masu yawan gaske. EFCC na tuhumar Saraki ne kan wasu biliyoyin nairori da aka wabcewa daga asusun gwamnatin jihar Kwara a lokacin da yake gwamnan jihar ana karkatar dasu zuwa wasu asusun karya wa?anda mallakin Saraki ne a ?oye. An ruwaito cewa akwai wasu kamfanoni da asusun bad-da-kama da Saraki ya rika amfani da su ana jibga masa ku?a?e a ciki…
Read MoreGwamnatin Bauchi Ta Bankado Dubban Ma’aikatan Bogi
Rahotanni daga Jihar Bauchi na bayyana cewar Gwamnatin jihar ta bayyana cewa ta gano ma’aikatan bogi 7,161 kuma ta cire su daga tsarin biyan albashi nan take ba tare da wani bata lokaci ba. Ma’aikatan bogin sun kunshi wa?anda ke aiki da gwamnatin jiha da kuma na ?ananan hukumomi da kuma yan fansho. Gwamnatin ta gano su ne bayan gudanar da bincike a shafin yanar gizo na ma’aikatan jihar baki ?aya, inda aka gaggauta daukar matakin da ya dace akai. Kwamitin binciken bisa jagorancin mataimakin gwamna, Sanata Baba Tela, sun…
Read MoreEFCC Ta Kama Tsohon Gwamnan Nasarawa Da Matarshi
Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta kama tsohon gwamnan jihar Nasarawa kuma sanata mai ci a yanzu, Tanko Al-Makura da matarsa bisa ga zargin cin amanar kasa. Majiyoyi daga hukumar yaki da rashawar sun shaidawa cewa a halin yanzu jami’an EFCC na yi wa tsohon gwamnan da matarsa tambayoyi a hedkwatar ta da ke Abuja. Duk da cewa ba a samu cikaken bayani kan dalilin kama tsohon gwamnan da matarsa ba, majiyoyi sun ce kamun na da nasaba da zargin cin…
Read MoreDa Yiwuwar Mutum Miliyan 85 Su Rasa Ayyukan Su A Najeriya – Gwamnatin Tarayya
‘Yan Nijeriya miliyan 85m za su rasa aikin su nan ba da jimawa ba saboda rashin wadatattun kayan aiki a ciki inji Ministan Karamin Ministan Kimiyya da Fasaha, Mohammed Abdullahi, ya bayyana cewa ‘yan Nijeriya miliyan 85 na gab da rasa aikin su saboda karancin ilimin zamani da fasaha. Ministan ya bayyana hakan ne a jiya a matsayin babban bako na musamman a wurin kaddamar da Generation Unlimited Nigeria, wani dandamali na duniya wanda ya hada kan gwamnatoci, cibiyoyi daban-daban, kamfanoni masu zaman kansu da matasa da nufin tallafawa matasa…
Read MoreKano: Majalisa Ta Bada Shawarar A Kama Rimin Gado
Majalisar dokokin Kano ta bu?aci a gaggauta kora da cafke shugaban hukumar korafe-korafe da ya?i da rashawa na jihar da aka dakatar Muhiyi Magaji Rimin-Gado. Kamfanin dilancin labaran Najeriya wato NAN ya ce majalisar ta yanke wannan shawarar ne bayan wani zama da ta yi ?ar?ashin jagoranta, Hamisu Chidari, a ranar Litini. A lokacin gabatar da rahoton, shugaban kwamitin wucin-gadi da aka na?a domin bincike akan zargin da ake yiwa Muhiyi, Musa Gama na jam’iyyar PDP ya shaida cewa mambobin kwamitin mai ?unshe da mutum 12 sun kammala bincikensu da…
Read MoreKano: Ganduje Ya Nada Sabon Shugaban Hukumar Yaki Da Rashawa
Rahotanni daga Jihar Kano na bayyana cewar Gwamnan JIhar Dr Abdullahi Umar Ganduje ya na?a Barista Mahmoud Balarabe a matsayin shugaban ri?o a hukumar ya?i da rashawa ta jihar domin maye gurbin Muhuyi Magaji Rimin Gado. Ranar Litinin da ta gabata ne Majalisar Dokokin Kano ta dakatar da Muhuyi Magaji daga shugabancin hukumar Kano na tsawon wata ?aya saboda wani ?orafi da ta samu a kansa daga ofishin Babban Akanta na jihar. Sai dai Muhuyi ya yi watsi da wannan zargi cikin wata hira da BBC ta yi da shi a baya-bayan…
Read MoreCin Amanar Kasa: An ?age Shari’ar Babachir Zuwa Watan Oktoba
Wata Babbar Kotu a Abuja ta ?age sauraron shari’ar zargin cin hanci da ake yi wa tsohon Sakataren Gwamnatin Najeriya, Babachir David Lawal, zuwa 6 ga watan Oktoban 2021. Ana zargin Babachir da aikata laifi 10 da suka ?unshi zamba da ha?a baki wajen karkatar da fiye da naira miliyan 544 mallakar gwamnatin tarayya da aka ware don nome ciyawa a yankin kudu maso gabashin ?asar. Kamfanin labarai na NAN ya ruwaito cewa hukumar ya?i da rashawa ta EFCC na tuhumar ?anin Babachir mai suna Hamidu da wasu mutum biyu…
Read More