EFCC Ta Fara Bibiyar Sawun Kwankwaso

Rahotanni daga Jihar Kano na bayyana cewar Hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta rufe wasu dukiyoyi mallakar Sanata Rabiu Kwankwaso a jihar Kano, cikin gaggawa ba tare da bata lokaci ba.

An ruwaito cewa daya daga cikin wadanda ke kusa lokacin da jami’an EFCC suka zo don rufe ginin ya yi tsokaci: Ya bayyana cewa jami’an sun shaida musu cewa rufewar ya biyo bayan wata takardar korafi da hukumar ta samu daga iyalan Ismaila Gwarzo, tsohon mai ba da shawara kan harkokin tsaro.

“Batun rufe gidan ya kasance lamari ne na kashin kansa tsakanin ‘yan gidan Ismaila Gwarzo kuma Kwankwaso ya shiga cikin lamarin ne saboda shi ya siya daya daga cikin kadarorin.”

Zuwa yanzu dai ba a ji ta bakin hukumar yaki da rashawar ba kan wannan sabon lamari.

A baya dai hukumar yaki da cin hanci da rashawar na binciken tsohon gwamnan bisa zargin karkatar da kudaden kananan hukumomi da suka kai biliyan N3.08. Mai magana da yawun hukumar ta EFCC, Wilson Uwujaren, ya tabbatar da cewa hukumar na binciken zarge -zargen da ke cikin takardar korafi.

Related posts

Leave a Comment