Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar tattalin arzikin Najeriya ya karu da kashi 5.01 a tsakanin watan Afirilu zuwa watan Yuni na 2021 daga kashi 0.51 da aka samu a watanni uku na farkon shekarar nan ta 2021.
Rahoton daukacin kayan aiki da kasar nan ta samar na watanni uku wanda NBS ta fitar a ranar Alhamis ya nuna cewa wannan cigaban na kashi 5.01% shine mafi girma da aka taba samu tun daga karshen shekarar 2014, Shekaru Bakwai.
Wannan habakar tattalin arzikin ya fi na wancan shekarar 2020 da ta gabata tare da ta watanni uku na farko na wannan shekarar da aka gani.
Rahoton ya ce wannan alamu ne na dawowar kasuwanci da al’amuran tattalin arziki bayan aukuwar muguwar annobar korona. NBS ta kara da bayanin cewa: Farfadowar tattalin arzikin kasar nan da ya fara daga karshen 2020, tare da dawowar al’amuran kasuwanci a gida Najeriya da duniya baki daya, shine silar cigaban da ake gani.
Kiyasi kan rahoton ya nuna cewa bangaren da ba na man fetur ba ya samar da kashi 6.74 inda sauran kashin an samo shi ne daga kasuwanci, yada labarai da sadarwa, sufuri da sauransu kamar yadda rahoton ya sanar.
