Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban ?asa, Muhammadu Buhari, ya roki matasan Najeriya su shiga sabon shirin “Jubilee Fellows Programme,’ wanda zai samar wa masu kwalin digiri 20,000 aikin yi.
Shugaban ya fa?i haka ne yayin kaddamar da shirin a fadarsa dake babban birnin tarayya Abuja, ranar Talata.
An ruwaito cewa shirin zai ?auki matasa wa?anda ba su haura shekara 30 a duniya ba, kuma zai kwashe watanni 12.
Mai taimakawa shugaban ?asa, Buhari Sallau, ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa shirin zai samar wa matasan aikin yi a wasu ?angarorin gwamnati da masu zaman kansu.
Shugaba Buhari yace: “Muna da yakinin cewa shirin zai samar da damarmaki ga matasan da suka kammala digiri kimanin 20,000 cikin watanni 12.” “Muna fatan wa?anda zasu amfana da shirin zasu yi amfani da damar da suka samu wajen yin abinda ya dace a watanni 12 da zasu shafe.”
“Wannan shirin zai taimakawa matasan Najeriya su samu kwarewar aiki da manyan kungiyoyi domin gina goben su ta ?angarori da dama da suka ha?a da fahasar zamani, kasuwanci, noma da kiwo da kuma ayyukan da suka shafi mu’amala da kudi.”
Shugaban ?asa yace gwamnatin ta maida hankai matuka wajen samar da ayyukan yi ga yan Najeriya a matsayin hanyar habbaka tattalin arziki.
A wani bidiyo da Buhari Sallau ya buga a shafinsa na facebook, Buhari yace: “?aya daga cikin kudirorin mu da muka fi baiwa muhimmanci shine samar da ayyukan yi ga yan Najeriya.” “Bayan an za?e mu a 2015, mun kirkiro da abubuwa da dama na samar wa yan Najeriya aikin yi.
“Mun ?auki yan Najeriya 500,000 da suka kammala karatu a shirin mu na N-Power dake karkashin tsarin jin kai da walwala.”
