Abuja: Kotu Ta Yi Fatali Da Bukatar Maina

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta ki sauraron bukatar belin tsohon shugaban PRTT, Abdulrasheed Maina.

Alkalin kotun Justice Ahmed Mohammed, ya ki sauraron sabuwar bukatar da lauyan Maina, David Iorhemba ya gabatar gare shi, na neman a bada belin tsohon shugaban hukumar kula da ku?a?en Fansho na ?asa.

Yayin da Iorhemba ya bukaci kotu ta bayar da belin tsohon shugaban PRTT, lauyan EFCC, A. M. Ocholi ya ce ya shigar da karar da ta ci karo da wannan bukatar.

Justice Mohammed ya bayyana cewa, ba shi da hurumin sauraron wannan bukatar yayin da kotu ta ke hutu. Alkalin ya bukaci a jira har sai Kotu ta dawo daga hutu lokacin da Justice Okon Abang zai dawo tunda dama shi ya fara sauraron shari’ar, sannan idan za su amince ko kuma su yi fatali da wannan bukatar.

Dama ana zargin Maina da wawurar dukiyar da ta zarce naira biliyan daya da sauran laifuka.

Tun ranar 25 ga watan Oktoban 2019 bisa umarnin Justice Abang, Maina yake tsare a gidan gyaran hali da ke Kuje. Daga baya aka sake shi daga gidan gyaran hali a watan Yuli bayan ya cika duk wasu sharuddan da aka bukata daga wurinsa.

A ranar 18 ga watan Nuwamban 2020 Justice Abang ya kwace belin Maina bayan ya karya wani sharadi na belin. Bayan nan, an kama shi a jamhuriyar Nijar kuma aka mayar da shi kotu a Disambar da ta gabata inda alkali ya bayar da umarnin a mayar da shi gidan gyaran hali da ke Kuje har sai an kammala shari’ar.

Related posts

Leave a Comment