Babu Wani Cigaban Da Najeriya Ta Samu A Tsawon Shekaru 40 – Sunusi

Tsohon Sarkin Kano Alhaji Muhammad Sanusi ll ya ce Najeriya ba ta samu wani cigaba ba cikin shekaru 40, na azo a gani tun daga kan mulkin shugaban kasa Shagari har zuwa yanzu.

Sanusi ya fadi haka ne a wani taron tattaunawa na murnar cikarsa shekaru 60 a duniya da aka gabatar ranar Asabar 14 ga watan Agusta 2021 a garin Kaduna.

Tsohon Gwamnan na Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ce akwai bukatar ci gaba a fannin tattalin arzikin kasa, amma abin ba?in ciki da takaici babu wani cigaba ta wannan fanni.

Ya ce duk da ya biya farashi saboda fadin gaskiya, ‘yan Najeriya sune suka biya ainihin farashi ta bangaren zama “cikin talauci, rashin tsaro, da hauhawar farashin kaya ”. A cewarsa:

“Lokacin da kuke cikin al’ummar da ba daidai take ba, ba za ki iya zama mai daidaita abubuwa ba, saboda idan duk kun daidaita, abubuwa ba za su canza ba.”

“Shekaru da yawa da suka gabata, lokacin da nake kururuwa akan biliyoyin da ake kashewa akan tallafin man fetur, na tuna an yi yunkurin kai hari gidana a Kano. Sannan ina CBN. Ina muke a yau?

Sanusi ya kara da jan hankali cewa: “Kira na makiyi ko mai sukar lamiri ba zai sa wadannan hujjojin su tafi ba. Don haka, duk inda muka je, dole ne mu fuskanci wannan gaskiyar. “Na yi kokarin kada in fadi da yawa, ba wai saboda babu abin da zan fadi ko saboda ina jin tsoron magana ba.

“Dalilin da yasa ban yi magana da yawa ba a cikin shekaru biyu da suka gabata shine saboda, ba ma sai na sake cewa komai ba, saboda duk abubuwan da muke gargadin su sun bayyana.

“A cewar Bankin Duniya, ina muke a 2019? A wannan adadin, a cikin shekaru biyu masu zuwa, dangane da daidaiton ikon siye, matsakaicin kudin shiga na dan Najeriya zai koma yadda yake a da tun 1980 a karkashin mulkin Shehu Shagari. “Wannan yana nufin a cikin shekaru 40, ba mu sami ci gaba ba; Shekaru 40 sun lalace a banza.

“Muna da nauyi a matsayin mu na mutane, mu tashi mu inganta rayuwar mutanen kasar nan. Idan gobara ta tashi, kowa ya tafi da likidiri don debo ruwan kashe ta. Muna bukatar fahimtar yadda tattalin arzikin mu ke aiki a matsayinmu na mutane; muna bukatar fahimtar zabin mu.

Related posts

Leave a Comment