Da Wuya A Daina Fasa Kwabrin Fetur A Najeriya – NNPC

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban kamfanin matatan man fetur na Nigeria, NNPC, ya ce kamfanin da wasu hukumomin tarayya za su cigaba da fama da kallubalen fasakwabrin kayayyakin man fetur saboda babancin farashin man fetur a Nigeria da kasashen da ke makwabtaka da ita.

An ruwaito Shugaban NNPC, Mele Kyari ya sanar da hakan yayin wani jawabi da ya yi wurin taron tattaunawa da kwamitin Majalisar Dattijai na tsara yadda ake kashe kudade ta shirya.

A cewar wata sanarwa da shugaban sashin hulda da jama’a na NNPC, Garba-Deen Muhammad ya fitar, Kyari ya ce akwai banbancin kimanin N100 a farashin kowanne lita daya tsakanin yadda ake sayarwa a Nigeria da kasashen da ke kewaye da ita hakan yasa yana da wuya hana fasakwabri.

Ya ce duk da cewa kamfanin na aiki da hukumomin tsaro domin ganin an yi magananin matsalar, har yanzu akwai sauran aiki duk da cewa ana samun cigaba. “Idan har akwai banbancin farashi sosai tsakanin yadda ka ke siyarwa da yadda ake samu a wani wuri, tabbas ka sani cewa zai yi wahala a magance matsalar.”

Ya jaddada cewa ayyukan masu fasakwabrin yasa yana da wahala a san takamaiman adadin man fetur da ake sha a kasar, yana mai cewa kamfanin kawai za ta iya sanin adadin da aka fitar da tashoshin dakon mai ne amma babu tabbas idan dukkansu ne aka yi amfani da su a kasar.

Related posts

Leave a Comment