Kamfanin NNPC Ya Lashi Takobin Inganta Rayuwar ‘Yan Najeriya

Kamfanin Mai na ?asa NNPC ya jaddada aniyarsa ta cigaba da inganta rayuwar al’ummar Najeriya da ababen more rayuwa da taimakawa wajen samar abin yi ga Matasa. Shugaban Kamfanin NNPC Malam Mele Kyari ya bayyana hakan lokacin da yake gabatar da jawabi a wajen taron tattauna albarkatun Mai da iskar Gas na shekarar 2021 wanda ya gudana a birnin tarayya Abuja. Mele Kyari ya kara da cewar Najeriya a matsayin ?asa mai yawan matasa ya zama dole ayi duba da samar da hanyoyin inganta rayuwar matasa a matsayin su na…

Read More

Dangote Bai Sha’awar Sayar Mana Hannun Jarin Matatar Mai – Shugaban NNPC

Babban Daraktan Kamfanin Mai na kasa watau NNPC, Mele Kolo Kyari, ya ce Aliko Dangote bai so ya saida musu da hannun jarin matatar da yake gina wa a garin Legas. Mele Kolo Kyari ya ce ya na da kyau kamfanin NNPC ya zuba hannun jari a kamfanin na Dangote, saboda gwamnati ta samu ta-cewa a matatar da ake gina wa. An ruwaito cewa shugaban NNPC din ya ce kamfanin na NNPC ya yi burin sayen kashi 20% na hannun jarin da kamfanin attajirin ‘dan kasuwan ya mallaka a garin…

Read More

An Bankado Kazamar Cuwa-Cuwa A Hukumar Kula Da Tashoshin Jiragen Ruwa

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Ofishin mai binciken kudi a gwamnatin tarayya ya sake aika wasu takardu zuwa ga Hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa NPA, ya na zargin hukumar da rashin gaskiya wajen harka da kudi. An ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta na zargin hukumar da yin aika-aika a shekarar 2018. Daga cikin zargin da ke kan wuyan shugabanninn Hukumar ta NPA akwai kin biyan hukumar FIRS harajin Naira biliyan 44.12 da yin facaka da Naira biliyan 88.23. Akwai haka-haka a kan kudin da aka kashe…

Read More

Pantami Ya Wakilci Nijeriya A Taron Kamfanin Wayoyin Zamani Na Duniya

Ministan Sadarwa da raya Tattalin Arziki na Tarayyar Nijeriya Sheikh Dakta Isa Ali Ibrahim Pantami ya jagoranci tawagar Nijeriya daga bangarorin gwamnati da na masu zaman kansu a taron “Mobile World Congress (MWC)” da ke gudana a garin Barcelona, dake kasar ??Spain. Kamfanin MWC babbar masana’antar samar da manyan wayoyi ce ta hannu da samar da abubuwan sabbin fasahohin zamani. Taron ya samu halartar masu wayoyin hannu na duniya, masana’antun na’urori, masu samar da fasaha, masu siyarwa, masu hannun jari, da sauransu. Duk a cikin kokarin Minista Pantami, na ganin…

Read More

Najeriya Za Ta Cigaba Ne Kawai Idan An Cire Tallafin Mai – Ministan Mai

Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur, Timipre Sylva, ya sake nanata bukatar sake fasalta sashen man fetur ta hanyar sanya farashin kayayyaki kamar yadda kasuwa ke bi don bunkasa tattalin arzikin kasar. Mista Sylva ya bayyana hakan ne lokacin da yake gabatar da jawabi a taron Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya (NAN) ranar Lahadi a Abuja. Da yake bayyana dalilansa na cewa dole a cire tallafin, ministan cewa ya yi: “Zan iya cewa matsaya ta a kan tallafin mai da sake fasali sanannu ne. Na yi imanin cewa domin wannar kasa ta…

Read More

Badakalar Biliyan 166: Majalisa Ta Yi Sammacin Hadiza Da Ministan Sufuri

Majalisar Wakilai ta tarayya a ranar Alhamis ta aike da takardar sammaci ga ministan sufuri Rotimi Amaechi da hukumar gudanarwa ta tashoshin jiragen ruwa dangane da ?atan dabo na wasu ma?udan ku?a?e da hukumar ta tara na haraji a shekarar 2016 da suka haura sama da naira Biliyan 166. Majalisar ta gano cewar wadannan ma?udan ku?a?e ba’a sanya su cikin lissafin kudaden da suka shiga asusun hukumar ma da sauran aikace-aikacen ta. Shugaban Kwamitin dake kula da asusun tarayya na majalisar Busayo Oluwole Oke ya fitar da takardar sammacin bayan…

Read More

Ta Faru Ta ?are: An Ingiza Farouk Lawan Kurkukun Abuja

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Tsohon shugaban kwamitin binciken tallafin mai a majalisar wakilan Najeriya ya shiga gidan yarin Kuje a Abuja inda zai kwashe shekara 7 bayan yanke masa hukunci a ranar Talata, bisa samunsa da laifin badakalar kudade.  An ruwaito cewa ba tare da ?ata lokaci ba aka tafi da Farouk Lawan gidan yarin Kuje bayan da kotu ta zartar masa da hukuncin ?aurin shekara bakwai a gidan yari. Wata majiya da aka ambato ta ce zai ci gaba da zama a gidan yarin har…

Read More

An Zo Wajen: Buhari Ya Kafa Kwamitin Kawar Da Talauci

Shugaba ?asa Muhammadu Buhari ya kaddamar da kwamiti na musamman don rage talauci a tsakanin yan kasar da kuma bijiro da dabarun bunkasa tattalin arziki. A cikin rahotonsa na baya-bayan nan, Bankin Duniya ya ce hauhawar hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya na kara talaucin da kuma tabarbarewar harkokin kasuwanci. Bankin ya ce kimanin ‘yan Najeriya miliyan 7 ne suka fada cikin talauci a shekarar 2020 saboda tashin farashin kawai. A wata sanarwa da Femi Adesina, mai magana da yawun shugaban, ya fitar a ranar Talata, an bayyana mataimakin Shugaban kasa…

Read More

Ma’aikatan Gwamnati Sun Fi ‘Yan Siyasa Cin Hanci Da Rashawa – Majalisa

Rahotanni daga zauren Majalisar Dattawa dake birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Kwamitin kula da kudaden gwamnati na Majalisar ya bayyana cewa sakamakon binciken da ya gudanar ya gano cewa ma’aikatan gwamnati sun fi aikata cin hanci da rashawa idan aka kwatanta da ‘yan siyasar kasar nan. Shugaban kwamitin Sanata Matthew Urhoghide, shi ne ya bayyana hakan a wata hira ta musamman da yayi da manema labarai a Abuja. Kwamitin wanda shi ne kadai kwamitin Majalisar Dattawa da tsarin mulki ya yi na’am da shi, a halin yanzu yana kan…

Read More

Al-Mundahana: EFCC Ta Gurfanar Da Manyan Jami’an Gwamnatin Sokoto Gaban Kotu

Rahotanni daga Jihar Sokoto na bayyana cewar Hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta gurfanar da ma’aikatan hukumar fansho ta makarantar firamare a kan zarginsu da ake da waskar da kudi har N553.985,644.1. Kudin an adana shi ne domin biyan malaman makaranta da suka yi ritaya kudin sallama da na fansho, inda Jami’an suka yi nasarar waskewa dasu. Ma’aikatan sun hada da: Abubakar Aliyu, Hassana Moyi, Haliru Ahmad, Kabiru Ahmad da Dahiru Muhammad Isa. An gurfanar da jami’an a gaban wata…

Read More

Babu Hujja A Bidiyon Karbar Dalolin Ganduje – Hukumar Yaki Da Rashawa

Shugaban Hukumar Hana Rashawa na Jihar Kano, Muhuyi Magaji ya bayyana cewa akwai dalilan da su ka nuna zai yi wahala a lokacin da aka nuno bidiyon da aka ce Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Ganduje ya ri?a cusa damman daloli a cikin aljifai a ce an bincike shi. Jaridar Daily Nigerian ce ta ri?a wallafa bidiyon ?aya bayan ?aya, wanda nan da nan ya zubar wa Ganduje mutunci a ?asa warwas. A ranar 12 Ga Yuni, Muhuyi Magaji ya bayyana cewa an rasa wanda zai fito ya yi aikin tare…

Read More

?angote Rahama Ne A Najeriya – Gwamna Bala

Rahotanni daga Jihar Bauchi na bayyana cewar Gwamnan jihar Sanata Bala Mohammed ya ce Aliko Dangote, shugaban kamfanin Dangote ya fi fahimtar ‘yan Najeriya fiye da wasu ‘yan siyasar kasar nan, kuma babu shakka shi rahama ne a Najeriya. Bala Mohammed ya sanar da hakan ne a Bauchi a ranar Talata yayin da jami’an gidauniyar Dangote suka ziyarcesa, a fadar gwamnatin jihar dake birnin Bauchi. Gwamnan ya kwarzanta biloniyan dan kasuwan a kan yadda yake tallafawa mata da masu bukatar taimako a kasar nan. “Ya bayyana jarumtarsa na mutumin da…

Read More

‘Yan Rashawa Na Barazanar Kasheni – Shugaban EFCC

Shugaban EFCC, wato hukumar dake ya?i da cin hanci da kar?ar rashawa na ?asa wato Abdulrashid Bawa ya bayyana cewa ana yawan yi masa barazan da rayuwar shi tun bayan da aka bashi shugabancin hukumar ta EFCC. Bawa yace lallai mutanen da suke ya?a bisa laifukan cin hanci suma suna maido da martani ta hanyoyi daban-daban. Shugaba Buhari ma ya ta?a yin irin wannan furuci a shekarar 2016. Shugaban EFCC yayi wannan jawabi ne yau talata a wata hira da aka yi shi a wani shiri na gidan talabijin ?in…

Read More

Talakawa Miliyan Guda Za Su Ci Moriyar Dubu Biyar-Biyar A Watanni Shida – Sadiya

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ‘yan Nijeriya miliyan ?aya da matsalar cutar korona ta shafa za su ri?a kar?ar Naira 5,000 a kowane wata har tsawon watanni shida. Ta ce wannan ya na cikin wani sabon shiri ne da ya fara aiki a farkon wannan shekarar da mutum 3,115 a Legas da Abuja, wanda yanzu za a fa?a?a shi zuwa sauran dukkan jihohi inda mutane za su fara amfana da shi su ma. Ministar Harkokin Jin?ai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ita ta bayyana haka a lokacin…

Read More

Kowane ?an Najeriya Zai Samu Miliyan ?aya Da Rabi A Watanni 6 – Sadiya

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ‘yan Nijeriya miliyan ?aya da matsalar cutar korona ta shafa za su ri?a kar?ar Naira 5,000 a kowane wata har tsawon watanni shida. Ta ce wannan ya na cikin wani sabon shiri ne da ya fara aiki a farkon wannan shekarar da mutum 3,115 a Legas da Abuja, wanda yanzu za a fa?a?a shi zuwa sauran dukkan jihohi inda mutane za su fara amfana da shi su ma. Ministar Harkokin Jin?ai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ita ta bayyana haka a lokacin…

Read More

Najeriya Za Ta Kasance Jagaba A Afirka Ta Fuskar Fasahar Zamani – Pantami

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Ministan sadarwa da tattalin arzi?in zamani, Dr. Isa Pantami yace Najeriya ta kai wani matsayi a yanzu ta fuskar fasahar zamani a jerin kasashen duniya, kuma tana da damar da zata samar da layukan waya da manyan wayoyin hannu ga ?asashen Africa. Ministan ya fa?i haka ne a wani taro da jam’iyyar APC ta shirya ranar Alhamis a Sakateriyar jam’iyyar dake Abuja. APC ta shirya taron ne ga hadiman gwamnati su baje kolin nasarorin da suka samu tun sanda suka shiga ofis…

Read More

Dalilin Da Ya Sa Ba Muyi Gwanjon Kayan Diezani Ba – EFCC

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau EFCC, Abdulrasheed Bawa, ya bayyana cewa kayan adon da suka kwace daga hannun tsohon ministar mai, Diezani Alison-Madueke ya kai N14.4 billion. Shugaban EFCC ya bayyana hakan ne ranar Juma’a yayinda ya gurfana gaban kwamitin majalisar wakilai dake bincike kan yadda akayi da kudaden satan da aka kwato, daga hannun barayin gwamnati. Yace “kayan adon da aka kwata daga wajen tsohuwar ministar ya kai na kudi N14.4 billion, kamar yadda…

Read More

Za A Yi Yajin Aiki Mafi Muni A Najeriya Idan… – ?ungiyar Kwadago

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Kungiyar kwadago ta kasa ba ta yi na’am da shawarar da kungiyar gwamnonin Najeriya ta bada na tsaida farashin fetur a tsakanin N380 da N408 ba. Inda ta bayyana cewar akwai neman takalo rigima da rashin tausayin al’umma a matsayar da kungiyar gwamnonin ta dauka na cewa a daina biyan tallafin Mai. Idan aka yi la’akari da halin da ‘yan Najeriya ke ciki, musamman ma’aikata, kungiyar kwadago ta ce bai dace a bada shawarar a kara farashin litar mai ba gaba ?aya…

Read More

Najeriya Ta Sake Karya Darajar Naira

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya karya darajar naira a hukumance sakamakon fara aiki da ya yi da sabon tsarin canji na Nigerian Autonomous Foreign Exchange (NAFEX). CBN ya rage darajar ku?in da kashi 8 cikin 100, inda yanzu take N410.25 kan kowace dala ?aya. Kazalika bankin ya bayyana sauyin ?arara a shafinsa. Mako biyu da suka wuce kamfanin labarai na Reuters ya ruwaito cewa bankin zai karya darajar naira ta hanyar sauka daga kan N379 kan kowace dala ?aya domin tsayar da farashin nairar guda ?aya a kasuwa. Wannan sauyin na…

Read More

Kamfanin Simintin Dangote Ya Tafka Mummunan Asara

Rahotanni daga masana’antar sarrafa Siminti ta kamfanin Dangote na bayyana cewar masu hannun jari a kamfanin Simintin Dangote sun yi asara a cikin wannan makon yayinda arzikinsa ya samu nuksani cikin kwanaki hudu. Masu hannun jari sun yi asarar N200 billion tsakanin Litinin da Alhamis. Wannan ya faru ne saboda tayin wawan da yan kasuwa ke yiwa hannun jarin kamfanin. Haka ya sa arzikin kamfanin ya sauko N3.5 trillion a ranar Alhamis, daga N3.7 trillion a ranar farkon makon. Hakan yana nufin an yi asarar akalla naira bilyan 200. Tun…

Read More