Bu?e Boda Ne Mafita Akan Tsadar Shinkafa – Rimingado

Hukumar kar?ar ?orafe-?orafe da ya?i da rashawa ta Kano, tace ta yi iya ?o?arinta wajen ganin ta magance ta’azzarar farashin shinkafa, sai da a wannan karon abin ya ci tura.

Shugaban hukumar Muhyi Magaji Rimingado ya ce ba zasu iya daidaita farashin shinkafa ba a yanzu domin matsalar ba daga masu samar da shinkafar ba ne.

“Hana shigo da shinkafar da gwamnatin tarayya tayi shine musabbabin da ya haifar da tsadar shinkafar, kuma gwamnatocin jihohi ba zasu iya ta?uka komai a kai ba.

“Gwamnatin tarayya ce ka?ai za ta iya kawo ?arshen matsalar ta hanyar bada dama a cigaba da shigo da shinkafar kamar yadda ake shigowa da alkama”. Inji shi

Rimingado ya bayyana hakan, ta cikin shirin Inda Ranka na gidan radiyo Freedom.

Related posts

Leave a Comment