Kano: Ganduje Ya Nada Sabon Shugaban Hukumar Yaki Da Rashawa

Rahotanni daga Jihar Kano na bayyana cewar Gwamnan JIhar Dr Abdullahi Umar Ganduje ya na?a Barista Mahmoud Balarabe a matsayin shugaban ri?o a hukumar ya?i da rashawa ta jihar domin maye gurbin Muhuyi Magaji Rimin Gado.

Ranar Litinin da ta gabata ne Majalisar Dokokin Kano ta dakatar da Muhuyi Magaji daga shugabancin hukumar Kano na tsawon wata ?aya saboda wani ?orafi da ta samu a kansa daga ofishin Babban Akanta na jihar.

Sai dai Muhuyi ya yi watsi da wannan zargi cikin wata hira da BBC ta yi da shi a baya-bayan nan.

Wata sanarwa Sakataren Ya?a Labarai na Gwamnatin Kano Abba Anwar ya fitar ta ce na?in Barista Balarabe ya fara aiki nan take, “sannan gwamna ya umarce shi da ya gudanar da aikinsa bisa doka”.

Kafin na?in nasa, Mahmoud Balarabe na aiki a matsayin mai shigar da ?ara a Ma’aikatar Shari’a ta JIhar Kano.

Related posts

Leave a Comment