Ma’aikatar Sadarwa Ta Tara Sama Da Tiriliyan Guda A Shekara Biyu – Pantami

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Ma’aikatar sadarwa da tattalin arzikin zamani tace ?angaren fasahar zamani (ICT) zai kara yawan ku?a?en shiga da yake samarwa gwamnatin tarayya domin habbaka tattalin arzikin ?asa.

Ministan sadarwa, Sheikh Isa Pantami, shine ya fa?i haka yayin zantawa da kamfanin dillancin labarai na ?asa (NAN) a Abuja ranar Lahadi.

Ministan ya jaddada amfani ICT wajen farfado da tattalin arzikin Najeriya, yace ?angaren na ICT shine yafi kowane ?angare cigaba cikin kankanin lokaci.

Minista Pantami ya kara da cewa Najeriya ta cigaba da tsammanin taka muhimmiyar rawa daga bangaren a nan gaba. Pantami yace: “Ku duba kididdigar da hukumar NBC ta fitar a sashen farko na shekatar 2021 (Q1), har yanzun ba’a fitar da na sashi na biyu ba; NBC ta bayyana cewa ?angaren ICT ya fi kowane ?angaren cigaba cikin sauri.”

“Shugaban ?asa ya fa?a cewa ICT ta taka muhimmiyar rawa wajen fitar da Najeriya daga karayar tattalin arziki.” “Idan ka duba ku?a?en shigar da muka zuba a asusun gwamnatin tarayya zaka tabbatar da haka. Wani lokacin sai da taimakawar ICT ake iya biyan albashi.

Dakta Pantami ya kara da cewa daga zuwansa ofis ?in ministan sadarwa zuwa yanzun bangaren ICT ya samar wa gwamnatin tarayya kudin shiga da suka kai tiriliyan ?aya.

Ministan yace: “Zuwa yanzun, bayan na kwashe shekara 2 a ofis, bangaren ICT ya samarwa gwamnati ku?a?en shiga da suka kai tiriliyan N1tr.” “Idan kuka duba kasafin ku?in ma’aikatar sadarwa, baya wuce biliyan N5bn. Mu muna samar wa ne mu baiwa wasu ma’aikatu su yi amfani da su.”

Related posts

Leave a Comment