Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Gwamnan jihar Malam Nasir El-Rufai, ya ce a shirye gwamnatocin jihohi suke su goyi bayan gwamnatin tarayya wajen cire tallafin man fetur baki daya. Jaridar Vanguard ta ambato gwamnan yana bayyana hakan ranar Talata a wajen gabatar da sabbin bayanai na Bankin Duniya reshen Najeriya da aka gudanar a Abuja. El-Rufai, wanda ya yi bayani ta intanet, ya ce idan ba a cire tallafin man baki daya ba, watakila jihohi 35 cikin 36 ba za su iya biyan albashi a shekarar 2022 ba. A cewarsa,…
Read MoreCategory: Tattalin Arziki
Tattalin Arziki
Tallafin Mai: Za A Rabawa ‘Yan Najeriya Dubu Biyar-Biyar
Labarin dake shigo mana daga Abuja babban birnin tarayyar Najeriya na bayyana cewar Gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta ce za ta raba wa ?an Najeriya tallafin sufuri na naira 5,000 a madadin tallafin mai da za ta janye gaba ?aya zuwa 2022. Ministar ku?in ?asar Zainab Ahmed Shamsuna ce ta bayyana haka a ranar Talata a wani taron Bankin Duniya kan ci gaban Najeriya. Ministar ta ce adadin wa?anda za su amfana da tallafin ya dogara ne da yawan abin da ke hannu bayan janye tallafin.…
Read MoreGwamnatin Tarayya Ta Fara Raba Wa Talakawa Kudade A Jigawa
Rahotanni daga Dutse babban birnin Jihar Jigawa na bayyana cewar Gwamnatin tarayya ta dawo rabon kudi N5,000 na shirin CCT na ma’aikatar jinkai da walwalan jama’a ga al’ummar Jihar Jigawa ranar Juma’a, 20 ga Nuwamba, 2021. An ruwaito cewa jama’a sun yi gangami a wuraren bada kudi a karamar hukumar Kiyawa ta jihar. A cewar rijistan rabon kudin, sama da talakawa mutum 167,620 ake sa ran zasu samu rabonsu cikin N1.6 billion. Rahoton ya kara da cewa mutane sun tafi wajen da katunansu domin karban kudi. Daya daga cikin wadanda…
Read MoreBabu Rigar Nono Ta Zinari A Kayan Da Muka Kwace Hannun Diezani – EFCC
Shugaban hukumar ya?i da rashawa EFCC Abdulrasheed Bawa ya musanta rahotannin da ke yawo cewa akwai rigar mama ta gwal a cikin kayan da hukumar ta ?wace daga hannun Diezani Alison-Madueke, tsohuwar ministar man fetur ta Najeriya. Ana zargin Diezani wadda ta fice daga Najeriya a 2015 da satar ku?in da suka kai dala biliyan biyu da rabi daga asusun gwamnatin ?asa a lokacin da take minista, kodayake ta musanta zargin. A watan Mayu ne Shugaban EFCC Abdulrasheed Bawa ya fa?a wa Majalisar Wakilai cewa darajar sarkoki da awarwaro da…
Read MoreBauchi: Gwamnati Za Ta Karbi Tallafin Biliyan 30 Don Kare Muhalli
Daga Adamu Shehu Bauchi Gwamnatin Jihar Bauchi zata karbo tallafin zunzurutun kudi kimanin naira Bliyan Talatin 30 daga Bankin duniya don kare muhalli daga gurbacewa a sanadiyan ambaliyan ruwa da yayi ma Jihar katutu a daminan bana da ta shige a mafi yawancin kananan hukumomin Jihar. Shugaban hukumar Kare muhalli na Jihar (BASEPA) Dr. Kabir Ibrahim ne ya shaida haka a lokacin aikin kwashe kasa da ya mamaye hanyoyi da gonaki a dalilin ambaliyan ruwan sama a Cheledi, cikin karamar hukumar Kirfi Ya ce maganan ambaliyan ruwa, ya daidaita wurare…
Read MoreShari’ar Buhari Da Gwamnoni: Dole Gwamnoni Su Biya ‘Yan Kwangila – Malami
Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Ministan Shari’a Abubakar Malami, ya shaida wa Gwamnoni 36 na Najeriya cewa al?alami ya bushe, tilas sai sun biya ‘yan kwangila dala miliyan 418 ?in da hukuncin kotu ya gindaya masu. Malami ya ce saboda haka gwamnatin tarayya ba za ta fasa fara cire dala miliyan 418 a hankali ba ta na dannawa asusun ‘yan kwangilar domin Kotu ce ta yanke hukuncin cewa a biya su ku?a?en. Kakkausan kalaman Malami sun zo ne mako ?aya bayan da wata Babbar Kotun Tarayya a…
Read MoreDangote Da MTN Ne Ke Sahun Gaba Wajen Biyan Haraji – Hukumar Tara Kudade
Kamfanin Simintin Dangote ya zama kamfanin da ya fi ko wanne kamfani biyan kudin haraji a Najeriya. Fittacen kamfanin mai kera siminti a Nigeria ya zama na farko cikin jerin kamfanoni 152 da hukumar kasuwanci ta Nigeria, NGX, ta lissafa a watanni shida na farkon 2021. A cikin watanni 6 na farkon 2021, Kamfanin Simintin Dangote da wasu kamfanoni 13 da ke kasuwanci a NGX sun biya harajin N289.4b ga hukumar FIRS da wasu hukumomin da ke samarwa gwamnati kudin shiga. Kamfanin Simintin Dangote ya biya gwamnatin tarayya zunzurutun kudi…
Read MoreDa Dumi-Dumi: Kotu Ta Daure Maina Shekaru 61
Wata Babbar Kotun Tarayya a babban birnin tarayya Abuja ta yanke wa tsohon shugaban kwamitin garanbawul a harkar fansho Abdulrasheed Maina hukuncin ?aurin shekara 61 a gidan yari amma zai yi zaman shekara takwas ne a gidan kason. Mai shari’a Okon Abang ya yanke wa Maina wannan hukunci ne kan laifuka 12 da suka ha?a da cin hanci da kuma halasta ku?a?en haram bayan shigar da ?ararsa da hukumar da ke ya?i da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon ?asa EFCC ta yi. Za a fara lissafa zaman gidan…
Read MoreTitin Dogon Kano Zuwa Maradi: Majalisa Ta Soki Amaechi
Kwamitin Ha?akar Sanatoci da Majalisar Tarayya masu lura da Sufurin Jiragen Ruwa da Jiragen ?asa, sun ragargaji Ministan Sufuri Rotimi Amaechi, dangane da abin da suka kira fifita Jamhuriyar Nijar a kan wasu sassan Najeriya. Amaechi ya sha ragargazar ce a ranar Alhamis, lokacin da ya bayyana a gaban Kwamiti domin kare kasafin 2022 na ma’aikatar sa. Tun da farko dai an fara tankiya ce a kan dalilin da ya sa za a gina titin Jibiya zuwa Mara?i na zamani, alhali kuma wanda za a gina daga Fatakwal zuwa Maiduguri…
Read MoreHukumar Kwastam Na Hankoron Tara Tiriliyan Biyu A Badi
Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Hukumar kwastam mai yaki da masu fasa-kauri tana shirin samun Naira tiriliyan biyu a matsayin kudin shigar gwamnati a shekara mai zuwa. Rahoton ya bayyana cewa mafi yawan wannan kudi za su fito ne daga iyakokin da ake da su a yankin kudu maso yammacin Najeriya, ana sa ran iyakokin Legas, Ogun, Ondo da kuma jihar Oyo za su kawo kashi 80% na kudin. Alkaluman da aka samu daga hukumar kwastam sun nuna jihohin nan hudu ne ke da alhakin kashi 80.48%…
Read MoreHukumar NDLEA Na Fama Da Fatara – Marwa
Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA), Birgediya Janar Buba Marwa (mai ritaya), ya koka kan rashin isassun ku?a?e a hukumar. Marwa ya bayyana cewa a lokacin da ya kama aiki a matsayin shugaban hukumar, daga gidansa ya dauko Talabijin zuwa ofis, domin samun saukin gudanar da ayyuka. Marwa ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a lokacin da ya bayyana a gaban kwamitin Majalisar Dattawa kan miyagun kwayoyi domin kare naira biliyan 38 na kasafin kudin…
Read MoreAn Maka Buhari Kotu Kan Batan Biliyoyin Kudi
?ungiyar SERAP mai fafutukar ya?i da cin hanci a Najeriya ta sake kai ?arar shugaba Buhari inda ta nemi kotu ta tilasta masabincikar zargin “bacewar sama da naira biliyan 881 a ma’aikatun gwamnati da hukumomi 367.” SERAP ta ce ta shigar da ?arar ne a babbar kotun Abuja kuma ta nemi a gano ku?a?en da suka salwanta tare da hukunta wa?anda aka samu da laifin salwantarsu. Ta ce gano ku?a?en zai taimakawa gwamnati maimakon kar?o rance. SERAP ta ce ta shigar da ?arar ne bayan zarge-zargen da ke kunshe a…
Read MoreBuhari Zai Ciyo Bashin Biliyan 82 Na Sayen Ragar Gidan Sauro
Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnatin Shugaban ?asa Buhari zata ciyo bashin bilyan 82 don sayen ragar kariya da cizon sauro a shekarar 2022. Wannan na kunshe cikin kasafin kudin da shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar gaban majalisar dokokin tarayya kwanakin baya. Sai dai anasu bangaren ‘Yan majalisar sun ce gaskiya ba zasu yarda da wannan abu ba, dole sai an sake dubawa. Majalisar dattawar Najeriya ta yi Alla-wadai da shirin da ma’aikatar kiwon lafiyan Najeriya ke yi na karban bashin $200 million (N82,070,388,916.76) a kasafin kudin…
Read MoreKalubalen Bashi: Jihohi 33 Ba Za Su Iya Biyan Albashi Ba
Rahoton dake shigo mana yanzu daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar mai yiwuwa jihohi 33 a Najeriya ba za su iya biyan albashi ba, saboda shirin gwamnatin tarayya na yanke kason kananan hukumomi domin fara yanke kudin da take biya na bashin dala miliyan 418 kwatankwacin naira miliyan 172 na kwararru kan kungiyar masu bayar da bashi ta kungiyar Paris Cub. Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, a rahotonta kan matsayin jihohi (‘State of States 2019′), BudgIT, wadda kungiya ce da ke sa ido kan harkokin kudi na gwamnati…
Read MoreBuhari Zai Kaddamar Da Shirin e-Naira A Gobe Litinin
Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kaddamar da Shirin Digital currency wanda ake kira eNaira, wanda shine alamar fara aiki da sigar dijital Naira(NGN) a Najeriya. A gobe Litinin 24/10/2021 Wata sanarwa daga Daraktan Babban Bankin CBN Bangaren Mista Osita Nwanisobi a ranar Lahadin da ta gabata ta ce kaddamar da eNaira ya samo asali ne daga babban binciken da babban bankin ya yi don saukaka tsarin mu’amala ga ‘yan Najeriya. Babban Bankin ya kuma fayyace cewa eNaira ba dandalin saka hannun jari bane amma sigar kudin zahiri ne, saboda ta…
Read MoreGwamnatin Tarayya Ta Ware Biliyan 104 Domin Sayen Jannareta
Mafarkin samun wadatacciyar wutar lantarki a Najeriya na kokarin gushewa kafin zuwan shekarar 2022 duba da yadda gwamnatin Buhari ta ware makudan kudi saboda saye da tattala janareta. Wannan ya biyo bayan matakin da ma’aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya suka shigar na kashe kimanin Naira biliyan 104 wajen sayen janareto, man fetur da yi musu hidima a shekarar 2022. Cikakkun bayanai na kunshe ne a cikin kudirin kasafin kudin shekarar 2022 wanda har yanzu majalisar dokokin kasar ba ta gama amince da shi ba. Gwamnatin Buhari ta ware miliyoyin kudi…
Read MoreKwastam Za Ta Kwace Jiragen Sama Mallakin ‘Yan Najeriya
Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Hukumar kwastam ta yi barazanar ?wace wasu jirage na ?ai?aikun jama’a 29 wa?anda masu su ba su biya kudaden fito ba. A wani rahoto da ta fitar kakakin hukumar Joseph Attah, ya ce idan ba su bayyana kansu domin biyan ku?a?en da ake bin su to za a ?wace jiragen cikin kwanaki 14. A ranar 31 ga watan Mayu kwastam ta sanar da shirinta na soma bincikar irin wadannan jirage a ?asar. An gudanar da binciken ne tsakanin 7 ga watan Yuni…
Read MoreDa Dumi-Dumi: EFCC Ta Damke Shugaban Rusau Na Kaduna
Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar wasu jami’an EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa, sun shiga hedikwatar hukumar KASUPDA da ke garin Kaduna inda suka yi babban kamu. An ruwaito cewa a safiyar Litinin din nan 11 ga watan Oktoba, 2021, aka ga ma’aikatan EFCC a hukumar KASUPDA, inda suka yi gaba da Darekta Janar na hukumar. Rahotanni sun ce EFCC tayi ram da shugaban hukumar, Malam Ismail Umaru Dikko. Zuwa yanzu babu wanda ya san laifin da ake zargin Dikko da aikata wa.…
Read MoreMatsalar Tsaro Ke Tilasta Najeriya Cin Bashi – Ministar Kudi
Gagarimar matsalar tsaron da ta dabaibaye Najeriya tare da dagula tattalin arzikin ?asar, kusan ita ce babban dalilin da ya sa ake yawan ciwo basussuka domin cike gi?in da ake samu a Kasafin Ku?a?e. Ministar Harkokin Ku?a?e Zainab Ahmed ce ta bayyana haka. A kasafin 2022 dai Najeriya na sa ran za ta samu ku?in shiga naira tiriliyan 10, yayin da ta kasafta kashe Naira miliyan tiriliyan 16. Wannan ya na nufin an samu gi?i kenan har na Naira tiriliyan 6, wa?anda Najeriya ta ce za ta cike sauran tiriliyan…
Read MoreDa Dumi-Dumi: EFCC Ta Tsare Uwargidan Gwamnan Kano
Rahotanni daga ingantattun majiya sun tabbatar da cewa hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin ?asa ta’annati, EFCC, ta tsare uwar gidan gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, a Abuja. A cewar majiyoyin, Hafsat Ganduje, wacce babban ?anta ya shigar da ?orafi a kanta, an gayyace ta don yi mata tambayoyi amma aka tsare ta ranar Litinin da daddare, watakila don ci gaba da binciken ne da safiyar Talata, Idan za a iya tunawa babban ?an gwamnan jihar Kano, Abdul’Azeez Umar Ganduje ne ya yi wa mahaifiyar tasa cune…
Read More