Rahotanni daga Jihar Bauchi na bayyana cewar Gwamnatin jihar ta bayyana cewa ta gano ma’aikatan bogi 7,161 kuma ta cire su daga tsarin biyan albashi nan take ba tare da wani bata lokaci ba.
Ma’aikatan bogin sun kunshi wa?anda ke aiki da gwamnatin jiha da kuma na ?ananan hukumomi da kuma yan fansho.
Gwamnatin ta gano su ne bayan gudanar da bincike a shafin yanar gizo na ma’aikatan jihar baki ?aya, inda aka gaggauta daukar matakin da ya dace akai.
Kwamitin binciken bisa jagorancin mataimakin gwamna, Sanata Baba Tela, sun mika rahoton kwamitinsu ga gwamna Bala Muhammed jiya a Bauchi.
