Kotu Ta Ba EFCC Damar Rike Miliyoyin Da Aka Wawure A Asusun Gwamnatin Tarayya

Rahotanni daga birnin Ikko na Jihar Legas na bayyana cewar wata babbar kotun tarayya mai zama a garin Legas ta zartar da cewa a karbe wasu kudi da aka karkatar daga ofishin hadimin shugaban kasa a mayar dasu ga Hukumar EFCC.

Ana zargin an yi awon gaba da N241m Alkali mai shari’a Nicholas Oweibo ya bada umarni a rike Naira miliyan 241 da aka yi gaba da su daga ofishin mai ba shugaban kasa shawara a kan harkokin siyasa.

Alkalin ya kuma yanke hukunci cewa a karbe wasu shaguna da ke kan layin Ekukinam, a unguwar Utako, birnin tarayya Abuja, da karin wasu ma?udan ku?a?en duk a mika su ga EFCC.

Mai Shari’a Nicholas Oweibo ya dauki wannan mataki ne bayan lauyan EFCC, Rotimi Oyedepo ya shigar da kara. Yadda aka tafka ta’adi a ofishin SDG.

Hukumar EFCC ta bakin Rotimi Oyedepo, ta fada wa kotu cewa an boye wadannan kudi ne kashi-kashi; N65m, N61m, N50, da N65 a wasu bankuna biyu a shekaru biyun da suka gabata.

Hukumar EFCC tace bincikenta ya nuna mata cewa an saye wannan shaguna da ke Abuja ne da kudin da aka karkatar daga ofishin mai ba shugaban kasa shawara.

Rahoton yace Abdulsalam Bawa ne babban akawu a ofishin hadimin shugaban Najeriyar. Ana zargin Bawa ya hada-kai da wasu ma’aikata aka yi satan.

Lauyan da ya tsaya wa gwamnati ya zargi wasu kamfanoni; Kouchdim Unity Nigeria Ltd da Lankass Global Ventures da hannu wajen wannan badakala. “Mun bankado akwai wani gida da aka saya da dukiyar jama’a da aka wawura, Abdulsalam Bawa ya ci amanar da aka damka masa.”

Related posts

Leave a Comment