Da Dumi-Dumi: EFCC Ta Yi Nasarar Kama Saraki

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar a yau Asabar ne hukumar EFCC suka cafke tsohon shugaban majalisar Dattawa, Bukola Saraki domin tuhumar sa akan harkallar wasu ku?a?e masu yawan gaske.

EFCC na tuhumar Saraki ne kan wasu biliyoyin nairori da aka wabcewa daga asusun gwamnatin jihar Kwara a lokacin da yake gwamnan jihar ana karkatar dasu zuwa wasu asusun karya wa?anda mallakin Saraki ne a ?oye.

An ruwaito cewa akwai wasu kamfanoni da asusun bad-da-kama da Saraki ya rika amfani da su ana jibga masa ku?a?e a ciki shi kuma yana ?iba ya na shagalin sa da su, wanda kuma ku?a?e ne na jama’a a lokacin yana gwamna.

Wa?annan kudade sun zarce tunanin mutum domin ku?a?e ne da ake wabtar su ana waskewa da su ana dan?arasu cikin wasu ?oyayyun asusu, shi kuma ya na kwasa yana shagalin sa da su.

Related posts

Leave a Comment